Jami’an Majalisar Dinkin Duniya UN za su kawo ziyarar aiki garin Maiduguri, Bama da Abuja a watan Oktoba

0

Ministan ayukkan harkokin waje Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa tawagar majalisar dinkin duniya za su ziyarci garin Maiduguri, Bama da Abuja a watan Oktoba domin karfafa aiyukkan agaji da akeyi a wasu bangarorin kasar nan.

Onyema ya bayyan zama da majalisar dinkin duniyar ta yi da wakilan gwamnatin Najeriya a New York kasar Amurka.

Ya ce majalisar dinkin duniyar za ta ziyarci Najeriya ne tare kungiyar bada agaji na OCHA domin hada karfi da karfe da gwamnatin Najeriya don ganin irin nasarorin da aka samu a ayyukan bada agaji.

” Sanin kowa ne cewa yankin arewa maso gabashin Najeriya ta yi fama da hare-haren Boko Haram inda a dalilin haka ne mutane da dama suka rasa rayukan su sannan wadanda suka tsira sun rasa abin dogaro da.

” A dalilin haka ne wadannan kungiyoyin bada agaji suka amince domin su tallafa wa mutane yankin da kuma sauran bangarorin kasar nan da suka yi fama da rikici.” Onyeama ya shaida.

Share.

game da Author