CIKAR NAJERIYA SHEKARU 58 DA SAMUN ’YANCI: Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari Dalla-dalla

0

CIKAR NAJERIYA SHEKARU 58 DA SAMUN ’YANCI: Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari Dalla-dalla

BA ZA MU BARI BOKO HARAM SU HANA YARANMU SAMUN ILMI BA

“A kowane lokaci, muna yi wa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa da iyalansu fata da kuma addu’o’i nagari. Bayan haka, muna sane da cewa manufofin Boko Haram sun hada da kame wurare da gurgunta sha’anin dimokradiyyar mu da hana ’ya’yan mu samun ilimi. Ba za mu taba lamunta su yi nasara a kan haka ba.

SADAUKARWAR JAMI’AN TSARON MU

“A daidai nan, zan so na yi jinjina ga sojojinmu mazansu da mata, ’yan sanda gami da sauran jami’an tsaro hada hukumomin tsare doka, wadanda ke ta gudanar da ayyukansu cikin mawuyacin hali don kare lafiyar kasarmu. A wannan hali, da yawa daga cikinsu sun sadaukar da rayuwarsu don kare kasa.

“A matsayina na shugabansu baki daya, ina mai tabbatar wa dakarun namu cewa zan ci gaba karfafa musu ta hanyar zurfafa kwarewarsu da samar musu dukkan kayayyakin da suke bukata domin ba su damar samun nasara a filin daga. Ina nan ina nazarin dukkan rahotannin da suka zo gabana dangane da hakkokinsu da na iyalansu.

“TSAFTACE YANKIN NEJA-DELTA

“Ba mu yi kasa a guiwa ba wajen kokarin tsaftace yankin Niger Delta, tare da saka wa matasan yankin kaimi da kuma sake farfado da harkokin rayuwa a yankin, za mu bunkasa su yadda ya kamata domin ba su tabbacin samun makoma mai kyau gare su da ma kasa baki daya.

YADDA ZA MU MAGANCE RIKICIN MAKIYAYA DA MANOMA

“Dadaddiyar matsalar nan ta rashin jituwa a tsakanin manoma da makiyaya wadda wasu masu son tarwatsa kasarmu suka haddasa ta, kawo yanzu an yi nisa da kokarin shawo kanta. Za mu ci gaba da mara wa kungiyoyi da gwamnatoci a matakin kananan hukumomi da jihohi har ma da shugabannin addini da na gargajiya baya, wajen samar da mafita ta din-din-din ga wannan matsalar.

“Da yake matsala ce da ake fama da ita a wurare daban-daban, mun hada hannu don yin aiki tare da kasashen da ke fama da irin matsalar domin tallafa mana. Da wannan, ina gargadin cewa duk wadanda aka samu da hannu a rikicin da sunan bai wa manoma ko makiya kariya, za su fuskanci fushin hukuma. Saboda haka muke kira ga dukkan ’yan Nijeriya masu son zaman lumana da su guji duk wani abu da ke da alaka da wannan rikici walau a cikin gida ko ketare don kuwa abu ne wanda ba shi da madogara a addini ko a kabilanci.

MATSALAR KAFEWAR TAFKIN CHADI

“Irin mummunan sakamakon da tsukewar Tabkin Cadi da kuma gurbatar da harkokin hakar mai ke haifarwa ga rayuwar jama’a da kuma harkokin rayuwa, wannan kadai ya isa mu yi gaba-gaba wajen kokarin samar tsaftataccen muhalli kuma mai inganci. Don haka za mu ci gaba da neman gudunmawa daga ketare don tallafa mana a wannan bangaren.

DAKILE CIN HANCI DA RASHAWA

“Muna ci gaba da samun tagomashi a harkar yaki da rashawa domin kwato kudade da kadarorin gwamnati da aka sace duk da irin tirjiyar da wasu ke nunawa. Abin kunyar da aka saba tafkawa a baya na wawure makudan kudade, babu shi a yau. Haka ma harkallar mai ba a bisa ka’ida ba da kuma kwangiloli barkatai da ba a aiwatar da su, hakan ya zama tarihi.

AYYUKAN INGANTA AL’UMMA

“Wannan kuwa abu ne da za a iya gani a zahiri cewa, mun iya aiwatar da ayyukan more rayuwa da dama da dan abin da muke da shi. Kamar hanyoyi da layin dogo da tashar jiragen sama da na ruwa, hakkin ma’aikata wadanda ke bakin aiki da ma wadanda suka yi ritaya, kula da manyan gadoji, fannin makashi da lantarki, makarantu, biyan bashin fanshon da muka gada da sauransu.

HABBAKA TATTALIN ARZIKI

“A yau, masu zuba jari na cikin gida da ketare na harkokinsu a Nijeriya hankali kwance. Mun dauke matakan da suka dace domin taimaka wa masu zuba jari da kuma nagartattun kwastomomi, matakan da za su taimaka mana wajen cimma bukatun da ake nema nan da wasu shekaru masu zuwa.

“Sannu a hankali muna muna karfafa tattalin arzikinmu ta hanyar kyautata darajar Naira. Muna kokarin gina tattalin arzikin da babu bukatar dogaro ga mai. A hannu guda, muna samun amfani gona mai yawa duk da kalubalen ambaliyar da ake fuskanta a wasu sassan kasar.

“Wadannan kyawawan sakamako kuwa, an same su a dalilin kwazo da aiki tukuru da muka nuna wajen kokarin cimma alherin da muka rasa tun bayan dawowar dimokuradiyya a 1999.

TASIRIN MATA A CI GABAN KASA

“Lamarin matasa na gabanmu a kowane lokaci. Saboda sun kasance ja-gaba a shaanin samun ’yancin kai. Sun fafata a fagen daga don tabbatar da hadin kan kasa. Sannan su ne suka yi gwagwarmayar raya dimokradiyya da kuma ’yancin dan-Adam a wannan kasa tamu a lokutan da neman hakan ke da hadarin gaske, musamman ma biyo bayan zaben 12 ga watan Yunin 1993 da na 2015 mai cike da tarihi.

“Ko a yau, matasa na da tasiri wajen cigaba da bunkasar kasar nan a dukkanin fannoni. Kama daga fannin fasaha da fannin noma, hakar madinai da sauransu. Baki daya, kokari muke wajen gina tattalin arziki mai dorewa.

“A tsakanin shekaru uku da suka gabata, mun samar da wasu tsare-tsare da shirye-shirye don bunkasa matasa don ba su rayuwa mai inganci. Mun amince da dokar nan ta bai wa matasa damar tsayawa takarar manyan mukamai, ta ‘not too young to run’, don bai wa matasa damar shiga a yi da su a harkar jagoranci da ma dimokradiyyar kasar mu.

SHIRIN CIYARWA A MAKARANTUN FIRAMARE

Shirin ciyar da yara a makarantun firamare an samar da shi ne domin karfafa wa yara shiga makaranta da kuma zuwa makaranta akan kari. Muna ci gaba da yin abin da ya kamata, domin tallafa wa kananan makarantu da jam’io’i wanda tuni an bada kudaden da za a yi amfani da su wajen samar da ingantattun kayan aiki, samar da shirye-shiryen bada horo don iya dogaro da kai hada da shirin tallafa wa mutanen da rikicin ta’addanci ya rutsa da su da ma wadanda harkar safarar mutane ta rutsa da su.

ILLAR SOSHIYAL MIDIYA NA BOGI

“Ba mu fuskanci irin wannan kalubalen ba a can baya. Don haka ya zama wajibi mu tashi mu yaki yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na zamani (soshiyal midiya) da suka saba wa manufofinsu. In ba haka ba, to fa dukkanin cigaban da muka samu tun bayan maido da dimokradiyya a 1999 za su bi ruwa kenan.

INGANTA HARKOKIN ZABE

“Na maida hankali matuka wajen ganin fannin zabe ya inganta ta yadda za a rika samun gudanar da sahihihan zabubbuka, wanda hakan zai bai wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa za ta amsa sunanta yadda ya kamata, a samu wadatar ma’aikata da kuma wadatattun kayan aiki.”

Share.

game da Author