Dan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar PDP, Jamilu Gwamna ya yi tir da zaben fidda gwani da aka yi a jihar a karshen makon da ya gabata.
Bisa ga sakamakon zaben da aka yi, Bayero Nafada ne ya lashe zaben fidda dan takaran da kuri’u 1,104 shi kuma Jamilu Gwamna ya tashi da kuri’u 147.
A bayanan da ya yi Gwamna ya ce sakamakon zaben da aka bayyana ba shine wakilan jam’iyyar suka zaba ba.
Yayi kira ga uwar jam’iyyar dake Abuja da ta soke zaben kwata-kwata.