Shehu Sani ne zai cira mana Tuta a zaben Sanata na shiyyar Kaduna ta tsakiya – Jam’iyyar APC ta Kasa

0

Jam’iyyar APC ta amince da sanata Shehu Sani ne shi kadai a matsayin dan takaran ta na shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zabe mai zuwa.

Idan ba a manta ba tun bayan darewar gwamnatin El-Rufai karagar mulkin jihar Kaduna suka sa kafar wando daya da Sanata Shehu Sani.

Abin ya kazanta da har tsinuwa suka rika jefar juna da. A haka dai a ka yi ta yi har ya kai ga gwamnan jihar ya daga hannun mai taimaka masa a harkar siyasa, Uba Sani da ya fito takarar kujerar.

Shehu Sani ya ki ficewa daga APC duk da cewa abokanan sa dake majalisa duk sun fice. Jam’iyyar APC ta sanar tun a wancan likaci cewa za ta saka wa wadanda suka yi wa jam’iyyar biyayya matuka.

Yanzu dai dan takara daya ne tilo jam’iyyar ta tantance kuma ta amince wa yayi takaran sanata ta shiyyar Kaduna ta tsakiya kuma wannan dan takara shine sanata Shehu Sani.

Ga sunayen Yan takararn sanatocin da ajam’iyyar ta amince su yi takara.

Share.

game da Author