KADUNA 2019: Isa Ashiru ya lashe zaben fidda gwani na PDP

0

Fitaccen dan siyasar nan kuma tsohon dan majalisar tarayya, Isah Ashiru, ya doke sanata Suleiman Hunkuyi, Sani Sidi da tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero a zaben fidda dan takara da aka yi a jihar Kaduna a karshen wannan mako.

Isah Ashiru ya lashe zaben ne da kuri’u 1300 inda Sanata Hunkuyi ya sami kuri’u 565 shi kuma Sani Sidi ya samu kuri’u 560.

Tsohon gwamna Ramalan Yero ya samu kuri’u 36.

Share.

game da Author