Zulum ya doke ministan Buhari da ‘yan takara 9 a zaben Barno

0

Shafaffe da mai kuma zabin gwamnan jihar Barno, Umara Zulum ya doke abokanan takarar sa nesa ba kusa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka yi a jihar Barno.

Ministan Makamashi da Ayyuka, Mustapha Shehuri da sauran ‘yan takaran sun sha kayin gaske a zaben.

Zulum ya samin kuri’u 4,432.

Wanda ya zo na biyu, kanin mataimakin gwamnan jihar Durkwa, ya sami kuri’u 115.

Kashim Imam, 20; Mustapha Shehuri, 1; Gambo Lawan 2; Atom Magira 2; Baba Ahmed Jidda, jakadan Najeriya a kasar Chana ya samu kuri’a 1.

Sauran ‘yan takaran, Umar Alkali, Abba Jato, da Umara Kumalia duk basu sami ko da kuri’a daya ba.

Kashim Imam, Umara Kumalia, Baba Ahmed Jidda, Abba Jato, Mustapha Shehuri duk basu halarci wurin da aka yi wannan zabe ba a Maiduguri.

Share.

game da Author