#ZABENOSUN: Yadda Jam’iyyun da ke fafatawa a zaben Osun suka fito da sabbin dabarun sayen kuri’u

0

Manyan jam’iyyun siyasa da ke fafutikar kokawar nasara a zaben gwamnan jihar Osun da ke gudana yau Asabar, sun shigo da sabbin dabarun sayen kuri’u daga hannun masu zabe.

Maimakon su rika raba kudi a sarari a wuraren jefa kuri’a, jam’iyyun sun sake dabarar rika rubuta sunayen wadanda suka jefa ko za su jefa musu kuri’ar, daga baya su biya su.

A kwanakin baya ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana soke amfani da wayar selula a cikin akurkin jefa kuri’a, ya ce ta yi hakan domin dakile harkallar saye da kuma sayar da kuri’u a ranar zabe.

Sai dai kuma wakilnan PREMIUM TIMES da ke lura da yadda zabe ke gudana a wurare daban-daban a jihar Osun, sun ga yadda aka shigo da wasu dabarun sayen kuri’a da sayar da ita a wurin zabe.

A wata mazabar Karamar Hukumar Ede ta Arewa, akwatin Unit 2, na mazabar 11, an ga wani ejan na jam’iyyar APC ya na rike da wata takarda da biro, wanda ya ke rubuta sunayen wadanda suka rigaya suka jefa kuri’a.

An kuma lura da yadda ya kan rika yin farat ya na kebewa wani wuri ya na karbar sunayen na su.

PREMIUM TIMES ta samu daukar muryar maganganun da mai rubuta sunaye da masu bada sunayen na su ke yi.

“Ka kuwa rubuta suna na?” Haka wata mata mai matsakaitan shekaru ta yi tambaya.

“Haba dai, na rubuta sunan ki mana. Ki je, ma hadu an jima.”

Sai dai kuma wakilinmu bai samu jin sunan mai daukar sunayen wadanda suka yi zaben ba.

Wakilan mu sun gano cewa an yi haka a rumfuna da dama, kuma har PDP da APC sun shiga cikin wannan daka-dakar.

A mazabun Unit 3, 5,4 duk wakilinmu ya ga ejan-ejan na APC da takarda da biro a hannayen su.

Wadanda suka san irin wainar da ake toyawa bayan karbar sunayen wadanda suka kada kuri’un su, sun bayyana wa wakilin mu cewa bayan an gama ana bin sunayen ne daya bayan daya ana kira an aba su dan hasafin kudade.

“Ba mu san ko nawa za a ba mu a wannan zaben ba. Amma dai a zaben baya, naira 500 aka rika ba kowa. A wasu wuraren kuma an ce har naira 2,000 an rika bayarwa.”

A rumfar zabe 005 da ke mazabar Ileeogbo kuwa, da idon wakilin mu ya ga ejan din wata jam’iyya na raba kudade a Karamar Hukumar Ayedere.

Wasu na cewa naira 2,000 ya kamata a ba su, amma an ba kowanen su naira 500.

Jami’an tsaro kuma sun kama wasu kananan yara biyu a wurin zabe, amma daga bisani aka bar su sukadangwala kuri’u suka yi gaba.

Share.

game da Author