Tawagar Kungiyar Tarayyar Turai (EU), ta kasashen Ingila da Amurka wadanda suka sa-ido a kallon yadda zaben gwamnan jihar Osun ya kaya, sun nuna matukar damuwar su dangane da “yawaitar katsalandan da aka rika samu jami’an tsaro sun yi yayin zaben.
Musamman sun nuna damuwa a kan yadda jami’an tsaro suka rika yi wa masu jefa kuri’a barazana, kama ‘yan jarida masu daukar rahoton yadda zabe ya rika gudana da kuma barazana ga kungiyoyin sa-ido kan tafiyar da zabe.
Wakilan sa-ido kan zabe daga wadannan ofisoshin jakadu uku, sun fitar da wata takarda ga manema labarai yau Asabar a Abuja, inda suka nuna cewa a gaskiya akwai bukatar jami’an tsaro su tsaya kan aikin su a lokacin zabe, maimakon su muna goyon bayan wani bangare, ko kuma takurawa da kuma cin zarafin wani bangare.
Sun ce hakan ya na da muhimmanci, musamman a lokacin zaben 2019 mai zuwa.
Zaben jihar Osun wanda jam’iyyar APC ta lashe, ya hadu da rikice-rikice, cin zarafin ‘yan adawa, ‘yan jarida da kungiyoyin sa-ido da jami’an tsaro suka yi a wurare da dama da kuma asarkala.
Ga Cikakken Jawabin Na Su:
“Tawagar sa-ido kan zaben-raba-gardama da aka gudanar a Jihar Osun, wadda ofisoshin Jakadun Kungiyar Tarayyar Turai, Ingila da Amurka ta tura a jihar, ta je kuma ta sa-ido sosai a kan yadda aka gudanar da zaben.
“Mu na kara jinjina wa al’ummar jihar Osun, ganin yadda suka fito sosai, suka jefa kuri’un su, damar da dimokradiyya ta ba su, kuma su ka fito ba tare da tayar da husuma ba.
“Sai dai kuma ba kamar yadda muka gano abubuwa marasa dadi da suka rika faruwa a ranar 22 Ga Satumba, yayin zaben-raba-gardama ba, a wannan rana, tawagar ta mu sun tabbatar da yadda jami’an tsaro suka rika yi wa masu jefa kuri’a barazana, kama ‘yan jarida masu daukar rahoton yadda zabe ya rika gudana da kuma barazana ga kungiyoyin sa-ido kan tafiyar da zabe.
“Su ma wasu magoya bayan wata jam’iyya sun bi sahun jami’an tsaro wajen yi wa magoya bayan daya jam’iyyar barazana.
“Akasarin abin da muka gani, wanda kuma shi ne za mu jaddadawa, shi ne cin zarafin da aka rika yi wa kungiyoyin kare hakkin jama’a, wadanda suka je domin aikin sa-ido kan yadda zaben zai gudana.
“Mun yaba da yadda shugabannin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), suka gudanar da zabukan.
“Amma a fili ya ke cewa katsalandan din da jami’an tsaro da kuma wasu ejan-ejan su ka yi, a ciki da wajen rumfunan jefa kuri’u, sun ishe mu zama wajibi mu fito mu yi kira kan muhimmanci da kuma bukatar tabbatar da cewa a 2019, an gudanar da zabe mai adalci, wanda ba murdiyya kuma babu bangaranci. Sannan kuma zaben ya kasance karbabbe kuma ingantacce da za a gudanar cikin kwanciyar hankali.
“Mu na kara yin kira ga jama’a a zauna lafiya, kuma duk wata tankiya ko kalubalantar sakamakon zaben da zai iya biyo baya, to a yi ta a cikin ruwan sanyi, ta hanyar da doka amince.
“Mu na kara jaddada matsayinmu cewa ba mu goyon bayan kowane bangare a cikin dukkan jam’iyyun da ke takara gaba daya. Mu na kan matsayinmu na masu goyon bayan baki dayan ’yan Najeriya, domin ganin an gudanar da zabe sahihi, karbabbe, babu magudi, babu murdiya, sannan a cikin lumana da kwanciyar hankali.”
Discussion about this post