ZABEN FIDDA-GWANIN GWAMNA: Takara Ko Takaddama a APC?

0

Ranar Lahadi 30 Ga Satumba ne ake gudanar da zaben fidda-gwanin gwamnonin APC a fadin kasar nan. Yau Asabar ne ya kamata a gudanar da zaben, amma sai aka daga zuwa gobe Lahadi. PREMIUM TIMES Hausa ta tsamo wasu jihohi da ta ke ganin duk yadda zaben zai kasance gobe, ba zai yi wa APC a matsayin jam’iyya dadi ba, sai ma ya kara kawo farraka da rabuwar kawunan manya da kananan ‘yan jam’iyyar.

Ta kuma dauko labarin yadda siyasar Yobe ke nema ta zama siyasar rakumi da akala.

ADAMAWA: Tsakanin Maigida da Mai Uwa a Gindin Murhu

Gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow ya na cikin tsaka mai wuya. Yayin da irin su tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha da sauran gagga suka hade wuri guda, a daya gefen kuma akwai surikin Shugaba Muhammadu Buhari, wato dan uwan uwargidan sa, Aisha, shi ma ya fito takara.

LEGAS: Sagwangwaman Karyewar Alkadarin APC a Kudu-maso Yamma

Irin yadda ake ta yi sa-toka-sa-katsi tsakanin jigon APC Bola Tinubu da kuma Gwamna Ambode, alama ce ta cewa akwai baraka a tsakanin APC.

Tinubu ya ki yarda a sake tsaida Ambode kai-tsaye, duk kuwa da cewa ana ganin babu gwamnan da ya kai shi aiki a cikin wadannan shekaru na mulkin APC.

An yi ban-baki, an bi da lalama, an yi magiya, amma Tinubu bai amince ba. Shi kuma Ambode ya yanki fom, shi ma zai tsaya takara tare da dan takarar da Tinubu ya ke so ya maye gurbin Ambode da shi.

Rahotanni sun ce shugabannin jam’iyya da shugabannin kananan hukumomi na bayn dan takarar Tinubu. Shi kuma Ambode ya na ta hada kan matasa a jikin sa.

Wannan ya sa ake gudun cewa kada fa Ambode yayi musu sakiyar da babu ruwa, idan suka riga shi kwantawa, to zai riga su tashi, ko kuma idan ya ga babu inda zai shimfida tabarmarsa ya kwanta, ya garzaya cikin PDP, tare da umartar dimbin magoya bayan sa cewa kowa ya yada zango inda ya shimfida tabarmar.

ZAMFARA: Ko Ta Ware Ko Ta Waraye

Akwai rudani da rikici sosai a jihar Zamfara, wanda ya tarwatsa kan jam’iyyar APC, tun bayan da Gwamna Abdul’aziz Yari ya nada wanda ya ke so ya tsaya takara, maimakon ya bari a yi zaben-fidda gwani, domin akwai manema kujerar gwamnan sosai.

Jim kadan bayan da Yari ya yi rabon mukaman da za a yi takara, sauran ‘yan takarar gwamna su bakwai, ciki har da mataimakin sa Ibrahim Wakkala, sun tubure sun ki yarda. Kuma duk suka yanki fom na neman fitowa takara.

Yari wanda ya dauko wani can daban ya ce shi zai yi gwamna, a bisa dukkan alamu, ya dauko ruwan dafa kan sa. Sauran ‘yan takara sun hade kai, kuma sun nuna sun fi Yari yawan jama’a.

A ranar da suka yi taro ne cikin makonni biyu da suka gabata, aka jefi tawagar gwamnan da duwatsu.

Shekaranjiya kuma sun sake yin wani gangamin taro, inda suka kara jaddada cewa za su tunkari gwamnan, “ko ta ware, ko ta waraye.’’ Kamar yadda Sanata Kabiru Marafa ya furta a wata hira da shi bayan kammala taron.

SALON YAKIN NEMAN ZABEN ZAMFARA:

Abin da zai fara zo wa mai saurare, shi ne zai yi tunanin taron wa’azin kasa ne na kungiyar Izala da aka saba yi. An bude taron da karatun Alkur’ani, sannan aka bi da addu’a. Daga nan kuma sai wani Alaramma ya rika sheka ruwan ayoyi, ana fassara su da halin siyasar da Zamfara ke ciki, da kuma irin halayyar Gwamna Yari.

Irin yadda Alaramman da ke jawo ayoyi ke fitar da karatu sigar karin harshen Malam Yahuza Bauchi, ya sa masu halartar taron gangamin siyasar rika yin kabbarori iyakar karfin su.

“Allahu Akbar!

“Allahu Akbar!

“Allahu Akbar!

Duk lokacin da mai jawabin ya dauko wani batu na rashinn adalci, rashin kyautawa da rashin gaskiyar da ya ke cewa Gwamna ya yi, sai ya jawo wata aya ya rafka wa gwamnan a kai.

Fara jan ayar ke da wuya, sai Alaramma ya karbe, ya karasa. Su kuma dubban jama’a a ranar ba maganar, kirarin jam’iyya, na “APC Canji”, sai dai “Allahu Akbar.”

Wakkala ya ce an ce gwamna na kiran su ‘banza-bakwai’, shi kuma ya jawo wata ayar Al’kur’ani, inda ya jefa kalmar ‘jahili’ a kan gwamnan.

Haka mai jawabin nan ya shafe sama da minti goma ya na yi wa gwamna Yari wankin babban bargo, tatas. Sannan ya rufe da sallama.

Ba wani ba ne wannan mai jawabin, sai mataimakin gwamna da kan sa, Ibrahim Wakkala, wanda duk wanda ya ji irin jawaban da ya yi akan gwamna, ya na mai nuna rashin amincewa da nada dan takarar gwamna da Yari ya yi, to ya san babu sauran shan inuwa daya a tsakanin mataimakin gwamna da kuma gwamna Yari.

Duk da cewa Sarkin Malaman Gusau, kuma Mataimakin Gwamna, ya yi wa gwamna sa tatas, inda ya rika amfani da ayoyin Alkur’ani wajen dagargazar gwamnan, kalaman da Aminu Sani Jaji ya yi a kan gwamnan sun fi kaushi, zafi, muni, kazanta da muzantawa. Wasu ba su buguwa a jarida.

Kamar yadda Wakkala ya rika sa Alaramma na jawo masa ayoyi ya na rafkawa a kan Gwamna Yari, ayoyin da aka rika jawo wa Aminu Sani Jaji ya na dankara wa Yari sun fi zafi da kuma ratsa jiki sosai. A ranar an nemi taken jam’iyyar APC a bakin mahalarta taron, an rasa, sai dai rurin kabbara, “Allahu Akbar!”, “Allahu Akbar’’!

PREMIUM TIMES HAUSA ta mallakai wadannan muryoyin kakaf, na duk wadanda suka yi jawabai a wurin taron. Sannan kuma ta samu kwafen wata hira da aka yi da Sanata Kabiru Marafa, inda ya ce ba za su amince da duk wani surkulle da Gwamna Yari zai yi gobe da sunan fidda dan takara ba.

YOBE: Siyasar Rakumi da akala

Gwamana Ibrahim Geidam ya hana mataimakin sa tsayawa takarar gwamna. Sai ya umarce shi da ya tsaya takarar sanata. Bayan da mataimakin ya amince, saboda tsananin biyayya, har ya yi nisa wajen kamfen, sai kuma Geidam ya umarce shi da janye takarar sanata din ita ma, ya dauki wani dan takara, ya dora.

Geidam kenan shi kadai tal ya dora dan takarar gwamna, ya tsaida ‘yan takarr sanata na shiyyoyi biyu, sannan kuma ya karbe takarar sanata da ke hannun tsohon gwamna Bukar Abba, ya bai wa kan sa Ibrahim ya bai wa kan sa.

Geidam na yin yadda ya ga dama a Yobe, shi ya sa ba mai iya nuna shi da yatsa. Kenan a Yobe dai APC ba za ta samu wata matsala ba a zaben-fidda gwani da za a yi gobe Lahadi.

Dalili kenan ma wani mai sharhi a ce asarar kudi kawai hukumar zabe za ta yi a jihar Yobe. Kawai a bai wad an takarar APC a huta, tunda PDP ta nuna kamar ba da gaske ta ke ba a jihar.

Kashim Shettima da ‘yan takarar APC a jihar Barno

A jihar Barno ma akwai irin wannan hayagaga a taakanin masu neman a tsaida su takarar gwamna a inuwar jam’iyyar APC.

Gwamnan jihar Kashim Shettima tuni ya nada wanda shi ya ke so ya gaje shi. Amma kuma hakan bai yi wa wasu da dama dadi ba.

Kanin Mataimakin gwamnan jihar Mamman Durkwa na daga jikin wadanda suka wasa wukar su domin fafatawa da zabin gwamnan.

Shima jakadan Najeriya a kasar Chana, ya bayyana cewa lokaci yayi ya zama gwamnan jihar Barno.

Shima dai yana cikin sawun wadanda zasu fafata a zaben fiddda gwamin ranar Lahadi.

Bayan su akwai ministan ayyuka Mustapha Shehuri da shima ke kan gaba wajen ganin an zabe shi dan takarar gwamnan jihar a APC.

Share.

game da Author