Za a fara jigilar dawowa da Alhazan jihar Katsina ranar 13 da 16 ga watan Satumba

0

Hukumar Alhazai ta jihar Katsina ta sanar wa alhazan ta dake kasar Saudi cewa za a fara jigilar su zuwa gida daga ranar 13 da 16 ga watan Satumba.

Hukumar ta ce bayan an kammala jigillar Alhazan ne za a fara jigillar ma’aikata daga ranar 18 ga watan Satumba.

Shugaban hukumar Salisu Ado da ya sanar da haka ya bayyana wa manema labarai ranar Laraba a garin Makkah cewa adadin yawan alhazan da za a yi jigilar su a wadannan ranakun sun kai 2,810.

Ado ya bayyana cewa sun yi wannan shela ne domin a kwantar wa alhazan jihar hankula ganin cewa an dan fara samun rashin jituwa da yanayi na kosawa a dawo gida.

A karshe Ado yaroki alhazan da su kara hakuri domin hukumar na iya kokarin ta wajen ganin kowa ya koma gidansa lafiya.

Share.

game da Author