Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana wani rahoto da ke nuna cewa yunwa na kara ta’azzara a kasashen duniya, sai dai kuma ta fi yin kamari a kasashen Afrika.
Rahoton ya ce daga cikin mutane miliyan 821 da ka gano su na fama da yunwa a cikin shekarar 2017, milyan 257 daga cikin su duk a Afrika su ke.
An fitar da wannan rahoto jiya Talata, inda ka ce kasashen Kudancin Amurka da Afrika ne suka fi fama da yunwa a cikin 2017.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan bincike ya nuna cewa yunwa na kawo babbar barazana ga shirin hukumar na tabbatar da kowa ya samu abinci, sannan kuma abinci mai gina jiki nan da shekarar 2030 a duniya.
Rahoto da kuma binciken ya nuna cewa a cikin shekaru uku da suka gabata, yunwa ta sake kunno kai har ta kai munin da ta taba kaiwa shekaru goma da suka gabata.
Ganin yadda abubuwa ke faruwa, Najeriya na kan gaba a sahun da kasashe masu fama da yunwa a Afika.
Rahoto ya nuna cewa a Najeriya akwai kananan yara ‘yan kasa da da shekaru biyar akalla miliyan 17.2 da ba su samun abinci ko abinci mai gina jiki.
Wani binciken da aka fara cikin 2016 aka kammala cikin 2017 ya nuna kashi 59 bisa 100 na kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar na fama da yunwa a jihohin Arewa maso Gabas da Najeriya
Boko haram ne ya ragargaza wannan yanki, ya haddasa yunwa ta yadda da dama mazuna yankin sundogara ne daga abincin da masu kai agaji ke kaiwa a yankin.