Yadda yajin aiki ke gudana a jihohin Sokoto, Kebbi da Kaduna

0

Kungiyar kwadago na jihar Sokoto ta bayyana cewa ma’aikata kalilan ne suka amsa kiran shiga yajin aikin gama garin da aka fara yau Alhamis.

Rahotanni daga Sokoto sun nuna cewa asibitoci da ma’aikatun gwamnatocin jihar da na tarraya a sun ci gaba da tafiyar da aiyukkan su kamar yadda ya kamata.

Sannan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da kuma Sakateriyar gwamnatin tarayya suma duk suna aiki a yau Alhamis.

Sai dai wasu ‘yan kungiyar NLC na jihar sun yi kokarin hana wasu ma’aikatan banki bude bankunan su.

Amma shugaban kungiyar Aminu Umar ya bayyana cewa kungiyar za ta sami hadin kan duk ma’aikata a jihar nan ba da dadewa ba.

‘‘Domin ganin hakan ta faru mun kafa kwamiti da za su tabbatar duk ma’aikata na bangaren gwamnati da masu zaman kansu sun yi na’am da yajin aikin.

Jihar Kebbi

A jihar Kebbi kuwa malamai sun kaurace wa makarantun gwamnati dake jihar.

Wani dalibin makarantar sakandaren Gwadangwaji dake Birinin Kebbi ya ce sun gaji ne da zaman jiran malaman su ne ya sa suke tafiya gida.

Wata malaman makarantar gwamnati Richeal Ngozi ta bayyana cewa dole suka kora yara gida domin kungiyar malamai ta Najeriya ta bada umurin duk malamai su zauna a gida.

A karshe ma’aikatan asibitin ‘Federal Medical Center’ dake Brinin Kebbi sun fara yajin aiki amma Sakatariyar jiha na gudanar da aiyukkan ta yadda ya kamata.

Jihar Kaduna

A jihar Kadun kuwa, kamar ba ama sanar da yajin aikin bane domin duk ma’aikatun gwamnati, makarantu, kasuwanni da da bankuna sun fito sun fito aiki.

Wata ma’aikaciyar jinya a asibitin Barau Dikko ta bayyana cewa kungiyar kwadago na jihar da kuma kungiyar ma’aikatan jinya basu sanar da su komai game da yajin aikin ba.

Ta ce za su shiga yajin aikin ne idan daya daga cikin kungiyoyin ta basu izinin haka.

Bayanai sun nuna cewa kungiyoyin ma’aikata da kuma kungiyar kwadago na jihar na tattauna yadda za su shiga wannan yajin aiki.

Share.

game da Author