Samar da wutan lantarki babbar matsala ce dake ci wa gwamnatin kasar nan tuwo a kwarya domin a yanzu haka kusan duk gidan da ka shiga zai yi wuya ba ka yi karo da janareta.
Wannan matsalar ya haifar da matsaloli da dama a Najeriya da ya hada da rashin aikin yi da gurgunta da sana’o’in da masana’antu.
Ya kamata gwamnati ta gaggauta daukan mataki wajen kawar da wannan matsala.
A haka ne ita ma fannin kiwon lafiya inda a yanzu haka asibitoci da dama na kokawa da matsalar.
PREMIUM TIMES ta zazzaga wasu asibitoci dake babban birnin tarayya, Abuja domin gano yadda cibiyoyin kiwon lafiya ke kawo wa ayyuka cikas.
Da farko dai wakiliyar mu ta ziyarci cibiyar kiwon lafiyar dake Abaji inda ta fahimci cewa rashin wutar lantarki na cikin matsalolin dake rage ingancin aiyukkan cibiyar.
Bincike ya nuna cewa cibiyar kiwon lafiyar dake Abaji asibiti ne dake kusa da mazauna garin Abaji musamman idan aka kwatanta nisar da babbar asibitin dake cikin garin Abaji din.
Ma’aikatan asibitin sun bayyana cewa rashin wutan lantarki, rashin isassun kudade da rashin kwararun ma’aikata ya hana asibitin bada ingantaciyyar kulan da ya kamata mutanen yankin su samun wanda hakan ya sa suka gwamace zuwa babbar asibitin dake cikin gari.
Ma’aikatan sun ce asbitin suna da kayan aiki, ruwan fanfo da kuma wurin ajiyar magunguna, da na rigakafi amma rashin wannan wuta ci musus tuwo a kwarya.
‘‘Mukan hada makonni kafin a kawo mana wuta a wannan asibiti, Janareto ne muke aiki da shi na tsawon awowi hudu duk rana sannan a hakan ma ba kullum ba.
” Mukan dai yi gwajin zazzabin cizon sauro, ciki, Hepatitis B, awon ciki, yin rigakafi da karban haihuwa amma duk a cikin duhu.
Wata ma’aikaciyar kiwon lafiya wanda aka fi sanin su da ‘Community Health Extention Worker CHEW’ mai suna Zuliaihatie Al-Hassan ta bayyana wa wakiliyar mu cewa duk da wannan matsalar da suke fama da shi basu koran marasa lafiya idan suka zo asibitin.
Daga nan kuma wakiliyar ta nausa cibiyar kiwon lafiyar dake garin Dakwa inda ta tadda aiyukkan kla da marasa lafiya na tafiya yadda ya kamata.
Ma’aikaciyar CHEW dake aiki a asbibitin Martha Zdikko ta bayyana cewa hakan na da nasaba ne da samun wutan lantarkin dake amfanin da hasken rana da wanda kamfanin VAYA ta tallafa musu da shi a shekaran 2016.
” A yanzu haka muna da lokacin wayar wa mazaunan kauyukan Gofina, KoKoife, Dakwa da Sarki kai game da mahimmanci zuwa asibiti musamman mata masu ciki da kuma wayar da kan mutane game da yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi.
Bayan haka jami’in hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na kasa (NPHCDA) Abdullahi Bulama yace a dalilin wadannan matsaloli ana samun karancin yin rigakafi a shiyyar Arewa Masu Tsakiya.
Yayi kira ga masu fada aji da a karkato da hankula zuwa ga wannan fanni da irin wadannan asibitoci domin samun inganci da raya asibitoci daceto raykan mutane.
A karshe ma’aikacin kiwon lafiya Abdulfatai Ibrahim y ace a ra’ayin sa samar da wutan lantarki wa cibiyoyin kiwon lafiyan dake birnin tarayya Abuja zai taimaka wurin yaye duk wadannan matalolin da gwamnati ke fadi tashi a kai.