Yadda mu ka tsira daga harin Boko Haram a sansanin sojoji – Mazauna Gudumbali

0

Wadanda ke da rabon ganin gobe, bayan da Boko Haram suka kai hari a sansanin sojoji da ke Gudumbali, cikin Karamar Hukumar Guzamala ta jihar Barno, sun bayyana yadda suka yi ido-da-ido da mutuwa, amma da ya ke su na da sauran kwana a gaba, sun tsallake, ba su sheka barzahu ba.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa wasu mahara ‘yan kungiyar Boko Haram cike da motoci ne suka kai wa wani sansanin sojoji hari dauke da manyan makamai.

NAN ta ce sai da aka shafe awa 12 ana fafatawa.

Wasu da suka tsira daga harin, sun bayyana wa NAN irin artabun da ya ritsa da su. Sun yi wannan bayanai ne yayin da suka tsira, suka tsinci kan su a Maiduguri.

BINTU BUKAR: “Ai ni ba zan iya bayyana irin firgitar da na yi ba ma. Ina jira ne kawai na ji sun karya kofar shiga gidan mu sun shiga sun kashe mu duka. Duk tsawon lokacin da ake ta harbe-harben nan ba ka jin komai daga karar bindigogi sai kuma kabbara, “Allahu Akbar!”

“Haka muka kwakkwanta a kan daben daki, gudun kada harsashi ya kauce ya samu mutum. Ba mu ji an daina harbe-harbe ba sai can wajen karfe 3 na asubahi.

“Daga nan ne fa muka fito kowa ya kama gudu. Na rike ‘ya’ya na uku kusa da ni, saboda a lokacin akwai sauran duhu, asubahi ba ta zo ba tukunna.

Sai kuma na tattaro wasu yaran makwauta na su biyar da su ma su ka gudo, duk na rike su kusa da ni.

“Mun ci doguwar tafiya fiye da kilomita 20, daga nan muka samu wata mota dauke da ‘yan gudun hijira wadda ta taimake mu zuwa garin Gajiram. To daga can ne aka karaso da mu nan Maiduguri.

“Sai dai har yau ban san halin da miji na ya ke ciki ba, ina cikin hali na razana sosai, domin ba zan taba son komawa Gajiram ba.

MODU BUKAR: Shi kuwa Modu Bukar, da zai tsere har da akuyar sa kama ya gudu da ita. Ya ce ya kasa gudu saboda ya na kula da iyayen sa masu matsanancin shekaru.

Bukar ya ce a lokacin da mu ka fahimci cewa maharan har fararen hula su ke kashewa sai ya kulle kan sa da iyayen sa a cikin gida da kwado.

“Sai da suka shafe sa’o’i da dama su na harbi kafin su fice su bar garin. Sun rika yin waka sun a cewa, “mun kama garin su gaba daya.”

Mun daina jin karar harbin bindigogi, amma sai aka shawarce mu da cewa mu zauna kada mu yi saurin ficewa daga gidajen mu.

A lokacin kuwa mun san hatta sojojin ma sun fice domin sun fa shafe zwa 12 su na gumurzu da Boko Haram.

“To da suka dawo ranar Asabar, sun dawo su na harbe-harbe. Sai muka raya a ran mu cewa sun dawo ne su karasa kisan fararen hula.

Ganin haka sai na bar iyaye na a gida ni muka na tsere. Sai da na yi tafiyar sama da kilomita bakwai a cikin duhun bishiyoyi daga nan na tsinci kai na a Gajiram. Daga can kuma na shiga mota na karaso nan Maiduguri a yammacin yau din nan.

AHMED USMAN:

Ya ce a lokacin da muka daina jin karar harbin, akasarin sojojin duk ba su nan.

“Yawancin mu dai manoma ne, kuma wadanda ke noma din duk sun yi amfanin gona a yankin na mu. Amma ba mu da mafita sai dai kawai mu jira har sai an sake tabbatar da zaman lafiya a yankin kafin mu koma tukunna.

Share.

game da Author