A wata sabuwar badakalar yi wa kasa hidima da PREMIUM TIMES ta bankado, Ministan sadarwa Adebayo Shittu ya kauce wa yi wa kasa hidima duk da ya kammala karatun sa na jami’a tun yana da shearu 25.
An haifi minista Adebayo Shittu ne a 1954 sannan ya kammala karatun sa na jami’a a jami’ar Obafemi Awolowo dake Jihar Osun tun yana da shekaru 25.
Tun daga wancan lokacin minista Shittu ya matse abin sa ya ci gaba da harkokin sa ta siyasa inda har ya kai ga zama minista Sadarwa a wannan gwamnati.
Tun Kafin nan Shittu ya rike mukamin dan majalisar dokoki a jihar Oyo.
Sai dai kuma ba kamar irin ta ministan Kudi Kemi Adeosun da ta zarce wurin ‘yan hada-hadar buga shaidun karya ba, Minista Shittu ya fito karara cewa lallai hakan ya faru amma sai dai shi ya dauka aikin sa da ya fara yi a wancan lokaci bayan kammala jami’ar sa ta isar masa bautar kasa.
Minista Shittu, ya kammala digirin sa ta farko a harkar Alkalanci ne a 1978 sannan ya tafi makarantar koyan aikin alkalanci. Ya zamo cikakken Lauya ne a 1979.

Doka ce a Najeriya da dole sai mai neman aiki ya nuna shaidar yi wa kasa bauta wato NYSC kafin a dauke shi aiki muddun ya kammala karatun sa ta digiri.
Hakan da Minista Shittu yayi zai iya kai shi zaman wakafi wato kurkuku.
Lauyoyi da suka yi mana karin haske kan abin da doka ya ce bisa kauce wa yi wa kasa hidima na NYSC sun bayyana cewa tabbas akwai matsalan gaske a abinda minista Shittu yayi.
Huwaila Mohammed da Abdul Mahmud duk sun bada sharhin cewa abinda yayi bai dace ba kuma saba wa dokar kasa ce.
Discussion about this post