A karo na biyu cikin makonni biyu, an sake samun rahoton wani soja da ya yi kumumuwar kashe kan sa, bayan da ya bindige wani sojan ya mutu.
Sojan dai kamar yadda PREMIUM TIMES ta samu labari, ya bude wutar ne a wani wurin atisaye na sojoji a Giri, kusa da Abuja, jiya Lahadi, ya kashe soja daya, ya ji wa wani rauni, daga baya kuma ya dankara wa bakin sa harsashi, har bakin radagargaje.
Abin dai ya fara zama abin damuwa ainun, ganin yadda hukumar tsaro ta sojoji ba ta bayyana irin wannan ‘shahadar kuda’ da sojojin ke yi su na harbe kan su.
Markus Yusuf ya kashe kan sa a Giri, wani gari can tsakanin Gwagwalada da Abuja, inda sojoji ke da wani matsuguni a wata gona. Haka wata majiyar cikin sojoji ta bayyana wa PREMIUM TIMES.
An ce ya na tare da wasu abokan aikin sa a wani filin da suke yin atisaye, kawai sai ya fara bude wuta, inda nan take abokan aikin duk suka watse.
Sai dai kuma harsashi ya samu wasu sojoji biyu, nan take daya yam utu, daya kuma ya samu mummunan rauni.
Sojan da ya ji raunin dai sunan sa Moses Gwakar, kuma kofur ne. Daga nan aka garzaya da shi Asibisin kwararru na Sojoji da ke Hedikwatar Tsaro, a Abuja.
An tabbatar da cewa lokacin da Yusuf ya yi kisan sannan ya kashe kan sa, ya na cikin maye ne, ya yi tatil da giya. Amma ba a san ko akwai wani dalili na sarari ko na boye ba.
An kira wayar kakakin hukumar tsaro ta sojojin Najeriya, amma bai dauki waya ba.
Discussion about this post