Wani Ardon Fulani ya nemi gwamnati ta kwace makamai daga hannun makiyaya a Jigawa

0

Lamidon Fulanin garin Zugobia da ke cikin Karamar Hukumar Guri a Jihar Jigawa, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada guiwa da gwamnatin jihar Jigawa domin ta raba wasu Fulanin daji makiyaya da makaman da ke hannun su.

Lamido Isa Adamu, ya yi wannan kira ne a wani taron wadanda ke nuna damuwa da irin zaman dardar da ake yi a yankin, inda suka taru a Guri domin tattauna hanyoyin kauce wa rikice-rikicen makiyaya da manoma.

Kwamitin Sasanta Rikici na Jihar Jigawa ne ya shirya taron wanda aka gudanar jiya Talata.

Ya ce wadannan makiyaya da suka fito daga Arewacin Bauchi, dama can sun saba zuwa daga lokuta daban-daban su na lalata amfanin gona, kuma su ka kai wa mutane hari.

Ya ki yarda da cewa wai mayar da burtaloli gonaki ne da aka yi ke janyo rigingimu tsakanin makiyaya da manoma. A nan Ardon cewa ya yi, wadannan makiyaya masu shigo, su na dai da wata boyayyar manufa kawai.

“Maganar gaskiya ita ce, wadannan Fulani masu shigo mana a nan Guri dauke bindigogi da takubba da kibau suke. Kuma daga Arewacin Bauchi suke shigowa, su na kai wa mutane hari tare lalata mana amfanin gona yadda ran su ke so.”

“Ai ba za a muna mana Fulatanci ba, domin mu ma Fulanin ne, amma wadannan mabarnatan da ke shigo mana baki ne. dalili kenan na ke kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha su shigo cikin wannan lamari su kwace wadannan makamai daga hannun su, tun kafin abin ya fi karfin hukuma.”

Sakataren Kwanitin Rabi’u Miko ya nuna cewa gwamnatin jiha ta samu wannan korafin ya je maya, kuma ta na kan tantance wuraren da manoma suka wuce iyaka, suke nome burtalolin da aka ware domin makiyaya su rika wucewa da shanun su.

Share.

game da Author