AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
To, ‘yan uwa shi dai arziki a musulunce ya kunshi dukiya ta zahiri kota ma’ana. Shi arzikin zahiri ya hada Zinare, Azurfa, Naiara, Dala…kadarori…amma arziki na ma’ana yakunshi Ilimi, Matsayi, Mukami, Basira, Iyali, ‘ya’ya, Halin Kwarai….
Lalle arziki abin nemane kuma ado ne, amma baya samuwa sai da dacewa daga Allah. “Arziki da ‘ya’ya kawar rayuwar duniya ne”( Alkahafi 46). Allah ya shar’anta mana nemen arziki, kuma ya shimfida mana hanyoyin neman sa, ta hanyar da zamowa cikin ibada, musamu lada kuma mu mori arzikin.
ABUBUWAN DA KE TAIMAKAWA BAWA WAJEN SAMUN ARZIKI
Allah da manzon sa sun yi umurni da neman arziki kamar babu mutuwa. Amma bin tafarkin Allah shi ne jagoran karowan arziki. Azikin bawa yana karuwa matukar bawa zai kiyaye wadannan abubuwa:
1. Bin dokokin Allah sau da kafa.
2. Takawa.
3. Yawan istigfari da tuba.
4. Yawaita Godiya ga Allah a bayyane da boye.
5. Aure da zuriya wani sanadi ne na karuwar arziki.
6. Sada zumunta.
7. Sadaka da ciyarwa don Allah.
8. Addu’ah
9. Karin Ilimi.
10. Dogaro ga Allah.
11. Yawaita zikiri
12. Tsare Sallar waduha.
13. haddar al-Kur’ani.
14. Yawan ibada.
15. Hajji da Umra.
16. Hijira da barin gida don neman arziki
17. Hakuri da juriya.
ADDU’O’IN NEMAN ARZIKI
1) ” اللّهُمَّ رَبَّنَآ أَنْزِلْ عَلَيْنَا مَآئِدَةً مِنَ السَّمَآءِ
تَكُونُ لَنَا عِيداً لأَوَّلِنَا وءَاخِرِنَــا وءَايَــةً مِنكَ
وَارْزُقْنَــا وَأَنْتَ خَيْــرُ الرَّازِقِيــنَ” .
2) يا الله يا رب يا حي يا قيون يا ذا الجلال والإكرام أسئلك باسمك
العظيم الأعظم أن ترزقني زرقا واسعا حلال طيبا برحمتك يا أرحم الراحمين.
3) اللهم رب السموات السبع ورب العرش العظيم إقض عنا الدين وإغننا من الفقر “.
“. اللهم إني أسئلك رزقاً واسعاً طيباً من رزقك ” 4)
Imam Bello Mai-Iyali, Kaduna.