Sojoji masu aikin fatattakar ‘yan ta’adda, sun kashe Boko Haram 14 tare da ceto mutane 146 daga hannun su. An yi wannan gumurzun ne a Gwoza ta jihar Barno a ranakun Lahadi da kuma Litinin.
Daraktan Yada Labarai na Hukumar Tsaron Sojoji, Texas Chukwu ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa baya ga mutanen da aka kubutar daga hannun Boko Haram, an kuma kubutar da dabbobin da suka kwace daga hannun su.
Chukwu, mai mukamin Burgediya Janar, ya ce ana nan ana tantance mutanen da aka kubutar din domin mika su ga hukumar da ta dace.
Sai dai kuma ya ce daga daga cikin jami’an sojojin ya samu rauni, amma ana ba shi kulawa a daya daga cikin asibitocin sojoji.
A wani labarin daban kuma, Chukwu ya ce sojojin Sashe na 3 na Operation Lafiya Dole, da aka girke a Karamar Hukumar Kukawa, sun kori ‘yan ta’addar da suka kai hari a garin.
Discussion about this post