Sani Sidi ya karbi fom din tsayawa takarar gwamnan Kaduna

0

Tsohon shugaban Hukumar NEMA, Sani Sidi ya karbi fom din tsaya takarar gwamnan jihar Kaduna a Inuwar Jam’iyyar PDP.

Tsohon kakakin gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero, Ahmed Maiyaki ne da ke tare da Sani Sidi a yanzu ya jagoranci tawagar zuwa ofishin jam’iyyar PDP a Abuja.

Mataimakin shugaban hulda da jama’a na jam’iyyar PDP ne ya mika wa tawagar Sani Sidi fom din a jiya Juma’a.

Idan ba a manta, tun a watan Agusta ne Sani Sidi ya bayyana ra’ayin sa na yin takarar gwamnan jihar Kaduna a taron dubban magoya bayan sa.

Tun bayan haka, Sidi ya zazzagaya kananan hukumomi 18 na jihar domin ganawa da wakilan jam’iyyar PDP.

Sani Sidi da ake ganin kamar shine zai iya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a jihar, saboda dattakun sa, kishi da sannin ya kamata zai gwabza ne da ‘yan takara kamar tsohon gwamnan jihar, Ramalan Yero, Sanata Suleiman Hunkuyi, Honarabul Isah Ashiru da wasu da dama.

Share.

game da Author