Safiya Abubakar ta lashe gasar rubutun gajerun labarai ta BBC Hausa, ‘Hikaya’ ta 2018

0

Wata malamar makarantar sakandire mai shekaru 29 da haihuwa, Safiya Abubakar ce ta lashe gasar rubutu da Sashen Hausa na BBC kan shirya duk shekara ga mata.

Safiya ce Tauraruwar Hikayata ta bana.

Tauraruwar ta lashe gasar ne da labarinta mai suna ‘Ya Mace.

Kamar yadda BBC Hausa ta wallafa a shafinta, alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana labarin ”Ya Mace’, a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.

Da take bayyana yadda ta ji bayan da ta samu labarin nasarar da ta yi, marubuciyar ta ce, “Lokacin da aka kira ni a waya aka shaida min labarina ya yi nasara, sai na rasa me ma zan ce.

“Sai da na sake duba wayata don na tabbatar ba mafarki nake yi ba, da gaske kira na aka yi aka shaida min na yi nasara.”

Ita dai wannan labara ta ‘Ya mace labari ne na wata budurwa mai suna Halima wadda ta shiga tasku bayan ta kai shekara 17 babu wani tsayayye, alhali a bisa al’adar gidansu da yarinya ta kai shekara 14 ake aurar da ita.

Matsin lambar da take fuskanta daga iyayenta da sauran dangi ya sa ta amince ta auri Garba duk da cewa ba a gudanar da wani bincike a kan shi ba.

Ga shi kuma mahaifinta ya ja mata kunne cewa kada ta kuskura a sake ta don idan ta dawo gida ba shi da halin daukar nauyinta.

Sanin hakan ya sa Garba yi wa Halima wulakanci iri-iri, har lamarin ya kai ga duka da zagi.
A karshe dai auren ya mutu; da ta koma gida mahaifinta ya kore ta bayan ya lakada mata duka, sannan ya sha alwashin tsine wa duk wanda ya ba ta masauki a cikin ‘yan uwa.

Wannan ya sa Halima ta yanke shawarar tsayawa da kafafunta ta hanyar kama hayar daki a cikin gari da yin ayyukan hannu don ciyar da kanta.

Sai dai ba a jima ba mai gidan ya samu labarin cewa ba ta da miji, ya ba ta notis yana mai cewa bai kamata mace irinta ta zauna a tsakanin mutanen kwarai ba.

A cewar alkalan gasar, kamar yadda BBC ta wallafa, wannan labarin ya ciri tuta ne saboda ya yi nauyi a galibin ma’aunan da aka yi amfani da su don tantance labarai 25 din da suka duba.

“Labarin ya tabo wata matsala da ke faruwa a wannan zamanin, inda iyaye ke Allah-Allah su aurar da ‘ya’yansu mata. Tun da aka fara labarin ake hawa, ake tashin hankali da jan hankalin mai karatu”, inji Bilkisu Yusuf Ali, daya daga cikin alkalan.

Jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya kara da cewa, “Matsalar labarin daya ce kawai: tun daga farko har karshe ake hawa, ba sauka. To amma shi wata dabara ce ta marubuta”.

A cewar shugaban sashen Hausa na BBC Jimeh Saleh, “Wannan gasa yaba mata murya cikin yanayi da maza ne suka fi shanawa sannan kuma an samu nasara sosai wajen ingancin labaran da mata ke rubutowa tun daga lokacin da aka fara wannan gasa.

Shugaban BBC na yankin Afrika ta Yamma, Oluwatoyin Ogunseye ta bayyana cewa za a karrama wadanda suka sami nasara a gasar a karshen watan Oktoba a Abuja.

Share.

game da Author