PDP ta maka Masari Kotun Koli

0

Jam’iyyar adawa PDP ta jihar Katsina ta maka gwamnan jihar Aminu Masari a gaban Kotun Kolin Najeriya inda ta nemi kotun ta haramta rantsatstsun shugabannin rikon kananan hukomomin jihar su 34 da gwamnan ya rantsar kwanan nan.

A cikin watan Agusta ne gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya rantsar da shugabannin rikon kananan hukumomi 34 da ke jihar.

Shugaban Jan’iyyar PDP na jihar Katsina Salisu Majigiri ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Talata, a Katsina.

Ya ce dama kuma jam’iyyar ta na da wani kwantai na karar da suka kai Masari a gaban Kotun Koli din tun a 2015 lokacin da ya rantsar da wadancan shugabannin riko bayan hawan sa mulki a lokacin.

“Tun farko sai da muka kalubanci wannan magaba a Babbar Kotun Katsina daga nan mu ne har Kotun Daukaka Kara ta Kaduna, amma gwamnatin jiya ta ci gaba ta sake nada wasu haramtattun shugabannin rikon kananan hukumomi.”

Majigiri ya ce su ma 23 daga cikin 34 da aka rushe sun kai kara a Babbar Kotun Jihar Katsina su na kalubalantar gwamnatin jihar.

Ya ce shugabannin kananan hukumomin da aka cire sun kai karar ce inda suka nemi a haramta wa Masari rantsar da shugabannin kwamitin da ya nada.

A karshe kuma a wani bangaren ya nemi gwamnatin jihar da ta bayar da rubutaccen bayanin yadda ta kashe kudaden jihar daga 2015 har zuwa yau.

Share.

game da Author