Mukamin siyasar Minista Shittu ba madadin aikin bautar kasar sa ba ne –NYSC

0

Hukumar Kula da Aikin Bautar Kasa (NYSC), ta yi watsi da ikirarin da Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu ya yi cewa mukamin siyasar da ya rike bayan ya kammala jami’a, shi ne madadin aikin Bautar kasa da bai je ba a shekarar har zuwa yau.

Kakakin Yada Labaran NYSC, Adenike Adeyemi ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke zantawa da jaridar Tribune.

Ta ce tsakanin mukamin mamba na majalisar dokokin jihar Oyo da Shittu ya rike a 1979 da kuma aikin bautar kasa, kowane zaman kan sa ya ke yi, babu mai zama a madadin daya daga cikin su.

Ta ce tunda dai Shittu ya kammala jami’a a lokacin da ya ke shekaru 26 a duniya, to ba a dauke masa zuwa aikin bautar kasa, NYSC ba.

Ana dauke aikin bautar kasa ne ga wanda ya cika shekaru 30 da haihuwa kafin ya kammala jam’ia zuwa sama.

Sauran wadanda doka ta yafe wa zuwa bautar kasa bayan kammala digiri, sun hada da wadanda suka tafi aikin soja, na dan sanda ko na jami’an leken asiri.

Wani lauya mai suna Abdul Mahmud cewa ya yi Minista Shittu kin zuwa aikin bautar kasa ya yi kawai ba wata kwana-kwana.

“Don haka ya karya dokar kasa kai-tsaye. Domin dokar cewa ta yi kafin a dauke ka kowane aiki, tilas sai ka yi bautar kasa, wato NYSC.”

“Dukkan wasu mukamai da ya taba rikewa ya yi aikin ne a bisa saba ka’idar dokar Najeriya. Don haka dukkan albashin da ya karba da sauran alawus a tsawon ayyukan da ya yi, sai ya amyo su. Kuma ya gaggauta sauka daga Ministan Najeriya.” Inji Mahmud.

Share.

game da Author