Man kifi baya hana masu cutar siga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya – Bincike

0

Wasu likitoci ‘yan kasar Britaniya sun gano cewa man kifi bashi da ingancin kare masu cutar siga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.

Jagoran binciken Louise Bowman ya ce sun gano haka ne a wani bincike da suka gudanar a jikin mutane 15,000 da basu dauke da ko wani irin cuta dake kama zuciya amma sun fama da cutar siga.

” Mun raba wadannan mutane gida biyu inda bangare daya muke basu maganin man kifi ‘Omega 3 capsules’ sannan dayan bangaren muke basu maganin man zaitun wato ‘Placebo Pill’.

” Bayan ‘yan kwanaki sai muka gano cewa mafi yawan wadanda muka basu maganin man kifi sun kamu da cutar dake kama zuciya sannan kalilan daga cikin bagaren dake shan maganin man zaitun ne suka kamu da wannan matsalar.”

A karshe Bowman ya yi kira ga masu dauke da ciwon siga kuma suke amfani da man kifi da su san da cewa man kifi baya kare su da kamuwa da cututtukan dake kama zuciya amma man zaitun na da ingancin yin haka.

Share.

game da Author