A yau Litini ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Tyopev Terna ya bayyana cewa wasu mahara sun kashe mutane 11 a kauyen Lopandet Dwei Du dake karamar hukumar Jos ta kudu.
Ya ce sanadiyyar wannan harin mutane 12 sun sami rauni sannan suna samun kula a asibitin koyarwa na jami’ar Jos da Plateau Specialist Hospital.
Ya ce harin ya auku ne ranar Lahadi da karfe 8:30 na yama.
” Ana sanar da mu aukuwar wannan hari, muka gaggauta ziwa wannan kauye, kafin mu kai wannan gari kuwa mun tadda maharan sun aikata abin da za u aikata sun gudu.
” A yanzu dai ba mu da masaniyar ko subwaye suka akai wannan mummunar hari.
Idan an kai wa Fulani hari, sai su zargi kabilan Berom, haka suma Berom din idan aka kai musu hari sai su zargi Fulani.
Wani shugaban kabilar Berom Jatau Davou ya bayyana cewa mutane 13 ne suka rasu a wannan hari.
” Ganau ba jiyau ba ya ce maharan sun far wa kauyen a kan babura, dauke da bindigogi sannan sanye da kayan sojoji.”
A karshe Terna yace sun aika da ma’aikatan su domin samar da tsaron a yankin.