Magidanci ya kashe matashi saboda naira 200 -’Yan sanda

0

An gurfanar da wani magidanci mai shekaru 34, a kotun Majistare ta Ebute Meta a Lagos a bisa, zarin ya kashe abokin fadan sa da adda, a kan naira 200 kacal.

An gurfanar da Olabiyi a gaban Mai Shari’a O.O Olatunji, inda ake tuhumar sa da hada baki da kuma kisa.

Ya shaida wa mai shari’a bai aikata abin da ake zargin sa da aikatawa ba. Shi kuma mai shari’a ya ce a ci gaba da tsare shi a kurkukun Ikoyi, har zuwa nan da kwanaki 30 da za a ciki gaba da sauraren karar.

Daga nan sai mai shari’a ya umarci a maida fayil din bayanan tuhumar da ake yi din ga ofishin masu gabatar da kara na gwamnati dimin su bayar da shawarar abu na gaba.

Tun da farko dai sai da mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata kisan ne a ranar 26 Ga Agusta da misalin karfe 6:30 na yamma, a gida mai lamba 23 da ke kan titin Irepodun, Shangisha, cikin unguwar Magodo.

Ya ce wanda ake zargin, shi da wasu mutane biyu da a yanzu haka sun tsere, sun kashe Akeem Ajilogba mai shekara 23 da a lokacin da suke wata tankiya a kan naira 200 kacal.

Mai gabatar da kara ya ce dokar jihar Legas ta 2015, mai lamba 223 da 233 ta shar’anta cewa wanda ya yi irin wannan kisan, shi ma hukuncin kisa ne kan sa.

Za a ci gaba da sauraren karar a ranar 11 Ga Oktoba, 2018.

Share.

game da Author