Kwastam za su fara bi gida-gida su na kwace shinkafar sumogal

0

Jami’an Kwastan sun bayyana cewa za su fara bi gida-gida su na zakulowa tare da kwace shinkafar da aka yi fasa-kwaurin shigo da ita cikin Najeriya a jihar Ogun.

A jiya ce kwastan suka ce za su rika bi cikin gidajen kwana, dakuna, shaguna, rumbunan adana kayayyaki da sauran kantuna domin su rika kwace shinkafar duk da aka yi sumogal din shigo da ita a jihar Ogun din.

Kwamandan Shiyyar, Micheal Agbara ne ya bayyana haka tare da cewa a cikin wata daya da ya gabata jami’an sa sun dakile ayyukan fasa-kwauri tare da samar wa gwamnatin tarayya makudan kudaden shiga.

Ya yi wannan jawabi ne ga manema labarai a kan iyakar Idiroko a yayin da ya ke bayyana wa ‘yann jaridar wani sabon salon aikin haka fasa-kwauci da za su fara ba da dadewa ba.

Ya fadi dalilin su na shirin fara kai farmaki a gidajen da cewa don su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen kokarin ta na bunkasa ayyukan noma a kasar nan, musamman shirin bunkasa noman shinkafa a nan gida, wanda zai rage dogaro da shinkafar waje.

Daga nan ya ce dirar mikiyar da za su fara a gidaje da kantuna da ma’ajiyar kayan abinci ta na da madogara daga dokar da ta kafa aikin kwastan, ba da rana tsaka suka yi nufin yin wannan gagarimin aikin kwacen shinkafar fasa-kwauri ba.

Daga nan sai ya ce za su fara wannan aiki kuma ba sani, ba sabo, duk wanda suka san ya kimshe shinkafar fara-kwauri sai sun fasa mabuyar sa sun kwashe ta.

Share.

game da Author