Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, wanda ke daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar nan a karkashin PDP, ya bayyana dalilan sa na zaben sirikin sa, Kabir Yusuf a matsayin wanda ya fi so ya yi takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2019.
Da ya ke hira da manema labarai jiya Litinin a Kano, Kwankwaso ya ce akasarin ayyukan da ya yi a lokacin da ya na gwamnan Kano a zango na biyu, duk kirkirar Kabir Yusuf ne, wato tsakanin 2011 – 2015.
Wannan ce hirar Kwankwaso da ‘yan jarida ta farko a Kano, tun bayan barin sa mulki a 2015.
Ya ce Kano ta na bukatar jajirtaccen mutum da zai yi aiki tukuru a matsayin gwamna, wanda zai gaggauta kawo ci gaban jihar, tare da jan ‘yann jam’iyya a jika.
“Ai da farko akwai mutumin da na nada kwamishinan ayyuka, amma tun da wuri sai na fahimci ba zai iya tabuka komai ba, ni kuma nan da nan na canja shi.
“Na kira Abba na ce zan ba shi kwamishina, amma ni aiki na ke so gagarimi. Don haka duk abubuwan da ku ka an gudanar a karkashin ma’aikatar ayyuka a jihar Kano a zangon mulki na na biyu, to Abba ne ya kirkiro su.
“Sannan kuma a halin yanzu Abba ya fi ni damuwa da ayyukan da aka watsar wadanda ba mu kammala ba kafin mu bar mulki, kuma wannan gwamnati duk ta yi watsi da su.
“Birnin Kwankwasiyya da muka fara, an yi watsi da shi, an yi watsi da Amana da Bandirawo duk mu mu ka fara su. Wannan gwamnatin ta yi watsi da aikin Gadar Jakara, an kauda kai daga titin Sheik Mahmud Salga Road, Gadar Sama ta Sabongari, wasu ayyuka a Jami’ar Northwest da sauran titina da dama da muka fara, amma duk wannan gwamnatin ta yi watsi da su. Kuma duk Abba ne ya kirkiro su.” Inji Kwankwaso.
Ya ce a zaben 2015 ya yanke shawarar zaben Ganduje ya fito takara ne, saboda a dabbaka ayyukan da aka faro tare. Kuma yin haka inji shi, don kada tafiyar Kwankwasiyya ta samu baraka ce a 2015.
Ya ce akwai hannun Ganduje a cikin akasarin wadannan ayyuka domin tare da shi aka rika yin yawancin su. Sannan kuma a lokacin idan Ganduje ya zama gwamna, to ya cancanta ne sosai.
Ya ce shi ya zabi Ganduje, ya ce masa, “Idan ban tsaida kai ba, to ba za ka shiga cikin gwamnatin ba kenan. Na farko dai kai ba kwamishina za ka sake yi ba, domin ka fi sauran girman mukami.
Kwankwaso ya ce amma a yanzu kafin ya zabi Kabir Abba Yusuf, sai da ya tuntubi magoya bayan sa ‘yan Kwankwasiyya sosai da sosai, ba da rana tsaka ya zabe shi kamar yadda ya yi na Ganduje ba a 2015.
Zaben da Kwankwaso ya yi wa Yusuf zama dan takarar gwamna a karkashin PDP a jihar Kano ya haifar da ka-ce-na-ce,. a gefe daya wasu ‘yan takara sun ki yarda har sun je Kaduna an tantance su. Ciki kuwa har da Salihu Sagir Takai.
Wasu kuma sun yi tsammanin cewa Kwankwaso zai nemi a tsaida tsohon mataimakin gwamnan jihar, wanda ya yi murabus saboda Kwankwaso, Hafiz Abubakar ko kuma Rabi’u Bichi.
Discussion about this post