Kwalara ta kashe mutane 61 a cikin watanni biyu a Yobe

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Yobe Muhammad Kawuwa ya bayyana cewa cutar kwalara ta yi ajalin murane 61 a cikin watanni biyu da suka gabata a jihar.

Kawuwa ya furta cewa a cikin wadannan watanni biyu mutane 906 suka kamu da cutar, 50 na kwance a gadajen asibiti sannan 61 sun rasu

” A da mun yi zaton cewa cutar amai da gudawa ne amma gwaji ya tabbatar mana cewa cutar kwalara ce ta bullo mana

Ya ce mutane 906 din da suka kamu da cutar mazaunan kananan hukumomi shida ne da suka hada Gujba, Gulani, Damaturu, Fune, Potiskum da Nangere.

Share.

game da Author