Wata kungiya mai suna NCAN ta siya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fom din takara.
Har yanzu dai Buhari ne dan takara tilo da ya bayyana ra’ayinsa na fitowa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC.
Kungiyar NCAN ta mika wa shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole chekin miliyan 45 da ta biya a banki don siyan fom din.
Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da jadawalin zaben fidda ‘yan takarar ta a zaben 2019.
A jadawalin kamar yadda babban sakataren shirye-shirye na jam’iyyar, Emmanuel Ibediro, ba saka wa hannu, za a fara tarukkan zaben wakilan da za su yi zabe fidda yan takara ne daga 12 ga watan Satumba.

Sannnan za a fara saida fom din neman yin takara a jam’iyyar daga 5 zuwa 10 ga watan Satumba.
Za a yi zaben fidda dan takarar shuagaban kasa na jam’iyyar ranar 20 ga wata sannan na gwamnoni ranar 26 ga watan Satumba.
1 – Za a fara saida da fom din neman tsaya takara daga ranar Laraba 5, ga wata – Litinin 10 ga wata.
2 – 13 – 14 ga wata kuma za a saurari korafe-korafe da ka iya tasowa a dalilin haka.
3 – Asabar 15 – Talata 18 ga wata kuma za a tantance ‘yan takaran da suka siya fom
4 – 19 – 20 ga wata kuma a saurari korafe-korafe.
5 – Za ayi zaben fidda dan takarar shugaban kasa ranar 20 ga watan Satumba.
6 – Za a yi zaben fidda dan takarar gwamna a jihohin kasar nan ranar Talata 25 ga wata.
7 – Sannan ranar 26 – 27 a saurari korafe-korafe da ka iya tasowa a dalilin haka.
8 – Ranar Asabar 29 ga wata kuma za ayi zaben fidda ‘yan takarar kujerun majalisar wakilai ta tarayya da na dattawa.
9 – Sannan a saurari korafe-korafen da ka iya tasowa a dalilin haka ranar a ranaku. 28 – 29 ga watan Satumba.
10 – Za ayi zabukkan kujerun fidda ‘yan takara na Babban Birnin Tarayya da sauraren korafe-korafen da ka iya tasowa a ranakun 2 ga watan Oktoba zuwa 3 ga watan.
Jam’iyyar ta ce dole duk dan takara ya maido fom din sa kafin ko ranar 12 ga watan Satumba.
Yadda kudin fom din yake
1 – Dan takarar shugaban kasa zai biya Naira Miliyan 45
2 – Gwamna – Naira Miliyan 22.5
3 – Kujerar Sanata – Naira Miliyan 7
4 – Majalisar Wakilai ta tarayya – Naira Miliyan 3.8
5 – Majalisar Dokiki na jiha – Naira 850,000.
6 – Nakasassu da mata zasu biya rabin abi da saura suka biya.
Bankunan da za biya kudin fom
Guaranty Trust Bank Plc- 013-727-6795
Zenith Bank Plc- 101-379-6249
Zenith Bank Plc- 101-367-8040
Zenith Bank Plc-101-400-8105
United Bank for Africa (UBA) Plc- 101-804-5285
Access Bank Plc- 069-298-8080
Unity Bank Plc- 002-312-2431.”
Discussion about this post