A cikin awa 24 APC ta canja ranakun zaben fidda ‘yan takaran ta sau biyu

0

A cikin awa 24 jam’iyyar APC ta canja ranaku yin zaben fidda ‘yan takaran ta sau biyu.

Wannan karon jam’iyyar ta danganta hakan da zaben Osun da za a sake yi a wasu mazabun da aka soke.

Idan ba a manta ba a ranar lahadi ne kakakin jam’iyyar Yekini Nabena ya fitar da takardar cewa jam’iyyar ta daga ranakun zaben fidda ‘yan takarar jam’iyyar, sai gashi kuma a yau litinin jam’iyyar ta sake sanar da daga ranakun zaben fidda yan takaran.

Zaben shugaban kasa ne za a fara yi wanda shugaba Buhari dan takara daya kwal tilo dama.

Jam’iyyar ta ce ta yi haka saboda kowani dan jam’iyya ya samu daman yin zaben.

Sabon ranar da za a yi zaben ya koma r28 ga watan Satumba wato ranar Juma’a kenan.

Share.

game da Author