Babbar Kotun da ke Abuja ta tsare wasu mutane biyar gidan kurkuku bayan da aka tuhume su da zargin laifin shigo da makaman da aka haramta, da kuma laifin yin fojare.
Mai Shari’a Sylvester Oriji, ya bada umarni a tsare Jude Ezirim, Chijioke Ogbuezi, Chidozie Okafor, Eze Uchendu da kuma Ozumba Uchenna a kurkukun da ke Kuje.
Ya bada umarnin tsare sun ne bayan da aka gurfanar da su a kotun sa jiya Litinin.
Sufeto Janar na ‘Yan sanda ne yi cajin su da zargin aikata laifuka uku da suka hada da shigo da makamai, fojare da kuma yin sojan-gona.
Daga nan sai ya bada umarnin cewa Mai Shari’a Maria Nasir ce za ta fara sauraren karar a ranar 6 Ga Satumba.
Tun da farko dai mai gabatar da kasa Malik Taiwo, ya shaida wa kotu cewa wadannan mutane biyar da kuma wani mutum daya da ya tsere, sun yi fojare na kamfanin wani mai suna Great James, Darakata na Great James Oil and Gas Ltd.
Taiwo ya ce sun yi hakan ne da niyyar shigo da kwantinar makamai a Najeriya a ranar 22 Ga Satumba, 2017, ba tare da sanin mai kamfanin ba.
Mai gabatar da karar ya ce mai kamfanin ne da kan sa ya kai korafin sojan gonar da aka yi da sunan kamfanin sa, ba tare da sanin sa ba.
Jami’an Kwastan na tsibirin Tin Can da ke Lagos ne suka kama su bayar sun yi kokarin fitar da kwantinar makaman daga tashar jiragen ruwa ta Tin Can.
Makaman dai daga kasar Turkiyya suka shigo da su.
Discussion about this post