Murabus din Kemi Adeosun ya samo asali daga yadda jaridar PREMIUM TIMES ta fara fallasa wata harkallar da Kemin ta rika yi tare da wasu shugabannin majalisa ana fitar da kudade daga asusun Gwamnatin Tarayya ana bai wa Majalisar Tarayya da ta Dattawa da sunan gudanar da ayyuka, ba tare da amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ba.
Ci gaba da wannan binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta rika yi, sai kuma ta sake gano cewa ashe Majalisa ta maida Kemi gugar yasar kudade ce saboda sun gano cewa takardar ta ta NYSC da aka ba ta shaidar yafe mata Bautar Kasa, ta bogi ce.
Baya ga cewa takardar ta bogi ce, sun kuma gano cewa an ba ta takardar ce bayan da ta cika shekaru 34, amma kuma ta kammala digiri tunn kafin ta cika shekaru 30 din da hukumar NYSC ta gindaya. Kenan idan za a bi ka’ida, sai Kemi ta je aikin bautar kasa kenan a yanzu,kuma sai an hukunta ta.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Majalisa ta rika yi wa Kemi wannan barazana. Saboda gudun kada a fallasa ta ne, sai ta rika biya wa shaugabannin majalisar dukkan bukatun kudaden da suka rika tambayar ta.
ASALIN KASHE-MU-RABAR KEMI DA SHUGABANNIN MAJALISA
Yadda Minista Adeosun, Saraki, Dogara da Akanta Janar suka yi wa Naira bilyan 10 rabon-tuwon-gayya
Wannan harkalla ba za ta yiwu a gina rami a rufe ta, ba tare da mun bankado ta ba. Mu na da hakkin da ya wajaba a kanmu, wato sanar da ‘yan Najeriya cewa wakilan su da ke Majalisar Tarayya, a karkashin shugabancin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, sun karbi zunzurutun kudade har naira bilyan 10 daga asusun gwamnatin tarayya ta haramtacciyar hanya.
Wadannan kudaden fa na musamman ne, wai malami da kudin kida, domin ba su ma cikin naira bilyan 125 da aka ware musu a cikin kasafin kudi na 2017 domin hidindimun su na yau da kullum.
Ku ma ba su cikin wasu naira bilyan 100 da aka ba su domin yin wasu ayyukan a-gani-a-yaba a mazabun su, wadanda ayyukan ma ba yi suke yi ba, in banda raba wa ‘yan bangar siyasa garmar shanu da dabura da injin markaden tattasai. Saura kuma su watsa aljihun su.
Wadannan naira bilyan 10 da ake magana a yanzu, sun isa a biya ma’aikata dubu 45 masu karbar naira dubu 18, albashin su na shekara daya.
An tabbatar da cewa kudin ba su ma cikin kasafin kudi, kuma Shugaba Muhammadu Buhari bai ma san an zurara kudaden cikin aljifan su ba.

Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ce ta amince kuma ta bada iznin ba su kudaden, kamar yadda ta umarci Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris, shi kuma ya cika aiki.
PREMIUM TIMES da UDEME sun ci karo da wannan barankyankyama yayin da suke bin diddigin yadda ake kashe kudaden manyan ayyukan gwamnatin tarayya.
An kamfaci kudaden an raba wa ‘yan majalisa a matsayin wani kaso daga cikin naira bilyan 50 da wai za a ba su domin su yi aikin a-gani-a-yaba a mazabun su.
Wadannan fa ba su cikin naira bilyan 70 daga cikin naira bilyan 100 da aka ba su cikin 2017, domin ayyukan a-gani-a-yaba a mazabun su.
Baya ga wadannan naira bilyan 10 da aka ba su, an kuma dumbuza wa Saraki naira milyan 485 shi kadai, domin ya gina kananan makarantun sakandare a shiyyar mazabar sa ta Kwara ta Tsakiya.
A cikin kasafin kudin 2017, an ce a bai wa Saraki naira milyan 450 domin ya gina makarantun, amma da ka tashi fitar da kudin, sai aka kara dora naira milyan 35, wato ribar-kafa, wai kura ta taka kwado a wurin farauta.
Saraki da Dogara sun kirkiro hanyar karbar kudin daga wurin Minista Adeosun a saukake ne ta hanyar ba ta sunayen wasu ‘yan kwangila har 82, wadanda Saraki da Dogara suka ce wai su na bin majalisa bashi, kuma suka rattaba adadin da kowanen su ke bin majalisa bashi.
Wannan ne kawai dalilin da suka yi amfani da shi a matsayin hujjar da Kemi ta sa hannu aka kamfatar musu kudaden.
Babu ruwan Adeosun, ba ta tsaya bata wa kan ta lokacin tambayar a kawo mata hujjojin ayyukan da ‘yan kwangilar suka yi ba, babu neman sauran hujjoji na zahiri da na badini ko ma daga Hukumar Tantancewa da Kula Da Kwangiloli ta Kasa, domin a ba ta satifiket na shaidar kammaluwar aiki.
Majiya da dama daga Ma’aikatar Harkokin Kudade sun tabbatar da cewa wannan harkalla ce kawai da kakuduba da kuma barankyankyamar da aka saba yi tsakanin ‘yan siyasa da ke kan mulki da kuma manyan ma’aikatan gwamnati.
Ita ma wata majiya daga Majalisar Tarayya ta tabbatar da cewa kudaden ba na wasu ayyuka ba ne, ‘yar-burum-burum ce kawai aka yi domin manyan wakilan majalisar su yi abin da Hausawa ke cewa gafiya-tsira-da-na-bakin-ki.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar da cewa kamfanoni 44 da Saraki da Dogara suka gabatar wa Kemi Adeosun daga cikin 82 din nan, ba su ma da rajista da Hukumar Kula da Kwangiloli ta Kasa, kuma babu su a cikin jerin Kididdigar ‘Yan Kwangila ta Kasa.
Karin bincike da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa wasu 17 ma daga cikin 44 din ko rajista da Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista ba su da ita.
Dukkan bangarorin Saraki da Dogara da PREMIUM TIMES ta tuntuba, sun kasa cewa komai.
Binciken da wakilinmu a Majalisa ya gudanar, ya tabbatar da cewa wasu ‘yan kwangilar a gaskiya sun yi ayyukan, amma fa tuni an rigaya an biya su tun tuni, amma kuma an jefa sunayen su a cikin wadanda aka ce wai su na bin bashi.
WATANDAR SAURAN CANJI NAIRA BILYAN 3.4
Yawanci an kamfaci kudaden ne ta hanyar yi wa kwangila daya biya sau biyu. Misali, Majalisar Dattawa ta biya kamfanin Messrs Quantita Services Limited naira milyan 115, alhali kuma a baya an biya kamfanin wata naira milyan 100 ta hanyar bad-da-bami da bad-da-kamar sunan aikin da aka yi.
An ba kamfanin Alik-Dove Services naira milyan 100 ladar aikin gyaran fitilun kan titin cikin majalisar tarayya. Alhali kuma shi ma kamfanin Quantita an ba shi naira milyan 50 a kwangilar aikin gyaran fitilun kan titin.
Duk yawanci an cire wadannan makudan kudade ne da sunan an sayo kayan ofis, gyaran ofisoshi, kula da su da kuma dakunan taro, kamar yadda takardar bayanan yadda aka yi watandar kudaden ta nuna.
An bayar da kwangilar naira milyan 33,918,750 ga kamfanin Popoona Star. Bayan an ciree kudin, sai kuma aka kara cire wannan adadin kudin da sunan kwangilar wancan aikin ga kamfanin Yujam Nigeria Limited.
Sama da kamfanoni 25 ne aka yi amfani da su aka rika karkatar da wuri-na-gugar-wuri har naira bilyan 3.4.
An kuma bayar da kwangilolin naira milyan 47, milyan 100, milyan 38, milyan 55.5 da kuma milyan 100 ga wasu kamfanoni daban-daban, wadanda babu takamaimen aikin da suka yi, ko kuma babu kayan da suka sayo domin a gani a tantance.
Baya ga wata naira milyan 454 da aka kashe wajen sayen kayan ofis, an kuma kashe wata naira milyan 100 wadda aka ba kamfanin Navadee Integrated domin kawo kayan aikin ofis.
HARKALLAR KEMI: Bori ya kashe bokanya
Lokacin da PREMIUM TIMES ta rika fallasa harkallar Kemi, wasu sun rika cewa bi-ta-da-kullin yarfen siyasa ne ake yi mata, wasu kuma ba su yard aba. Ita kan ta Kemi da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da na Tarayya, Yakubu Dogara, duk sun karyata labarin, har ma wasu suka yi barazanar kai PREMIUM TIMES kasa kotu idan ba ta janye labarin ba. Kamar yadda za ku karanta barazanar da su ka yi wa wannan jarida a lokacin da ta fara fallasa harkallar:
Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun maida martani ga PREMIUM TIMES dangane da labarin da aka buga jiya safiyar Juma’a, mai take: “Yadda Minista Adeosun, Saraki, Dogara da Akanta Janar suka yi wa naira bilyan 10 rabon-tuwon-gayya.”
Da ta ke maida martani, Kemi Adeosun ta bayyana labarin da aka buga da cewa “karya ce, kuma ba a yi bincike ba.”
Kakakin yada labaran ministar, Oluyinka Akintunda, ya bayyana cewa sun yi mamakin ganin yadda PREMIUM TIMES ta buga labarin a matsayin minista ta bayar da kudaden ba bisa kan ka’ida ba.
A cikin wata takarda da ya sa wa hannu a madadin ministar, Akintunda ya ce kudaden da ministar ta bayar duk kan ka’ida aka bayar da kudaden, kuma har ma sai da Kwamitin Duba Cancantar Biyan Kudade ya zauna ya duba, kafin a biya kudin.
“Ministar da kan ta ce ma shugabar kwamitin, don haka kuma kafin ta bada umarnin a cire kudaden, sai da aka aiko mata da takardar neman a fitar da kudin, ba haka kawai da ka ta fitar da su ba.”
Ministar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da abin da PREMIUM TIMES HAUSA ta buga, ta na mai cewa “labarin bogi ne.”
Sai dai kuma ministar ba ta ce komai ba dangane da yadda ba a gabatar mata da bayanan da ke nuna an yi kwangilolin ba, sai kawai ta ce a fitar da kudin, kuma ba ta ce komai ba dangane za ikirarin PREMIUM TIMES HAUSA, cewa kamfanoni 44 daga cikin 82 da aka bada sunayen su a matsayin wadanda suka yi kwangilar, duk na cuwa-cuwa ne.
Har ila yau, minista Kemi Adeosun ta yi shiru daga bayanin da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi cewa yawancin kwangilolin duk an yi su, amma kuma an rigaya an biya kudaden tuni, sannan daga baya kuma aka kara rattaba sunayen su aka kara biyan kudin da sunan su.
SAI NA MAKA KU KOTU – Saraki
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya yi barazanar maka PREMIUM TIMES kotu dangane da labarin da aka buga, inda aka fallasa yadda suka yi wa naira bilyan 10 rabon-tuwon-gayya.
Shi ma ya maida martani a jiya Juma’a da yamma bayan an buga labarin.
Kakakin yada labaran sa, Yusuph Olaniyoni, ya fitar da sanarwa inda Bukola Saraki ke ta jaddada cewa bai karbi wasu kudade naira bilyan goma ta haramtacciyar hanya ba.
Ya ce duk kudaden da aka karba, an karbe su ne ta sahihiyar hanya. Kuma bangaren da wannan alhaki ya rataya a wuyan sa, shi ke karbar kudin ba Saraki ko Dogara ba.
Ya ce labarin da aka buga karya ce kuma an nuna rashin iya bincike a cikin labarin.
Sai dai ya tabbatar da cewa ya na da masaniyar za a buga labarin, domin an tuntube su domin a ji ta bakin sa, tun kimanin makonni uku da suka gabata.
Ya ce an hada PREMIUM TIMES da bangaren majalisa masu kula da gudanar da ayyuka a majalisar, inda bangaren ya ce a saurare su, za su bada amsa.
“Mun yi mamakin yadda PREMIUM TIMES ta yi gaggawar buga labarin, ba tare da jiran amsar da za a ba ta ba.”
Shi ma Saraki ya yi kira da kada wanda ya dauki labarin a matsayin gaskiya, karya ce kawai da kitsa sharri, kuma ya ce zai garzaya kotu tunda abin ya kai ga bata masa suna.
Sai dai shi ma kamar Minista Kemi, bai ce komai ba dangane da batun barankyankyamar kamfanonin bogi da kuma yadda aka biya kudaden da sunayen wasu kamfanonin da an rigaya an biya su kudaden aikin da suka yi tun can baya.