KANJAMAU: Matasa ‘yan shekaru 10-25 sun fada hadarin kamuwa da cutar a Najeriya

0

Gwamnatin tarayya tare da hadin guiwar Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da asusun kula da bada tallafi na (UNICEF) sun kirkiro da shiri domin dakile yaduwar cutar kanjamau a tsakanin matasan kasar nan.

shirin dake da taken ‘Adolescents and Young People (AYP) HIV Prevention Campaign’ shiri ne wanda zai taimaka wurin wayar da kan matasa musamman masu shekaru 10 zuwa 24 kan cutar kanjamau.

Gwamnati ta dauki wannan matakin ne bisa ga sakamakon binciken da WHO ta gudanar da ya nuna cewa adadin yawan matasan dake kamuwa da cutar kanjamau a kasar nan na karuwa.

” Bincike ya nuna cewa daga cikin mutane miliyan 2.1 dake dauke da cutar kanjamau a kasa Najeriya, 240,000 matasa ne masu shekaru 10 zuwa 24.

A dalilin haka ne shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) Sani Aliyu ya ce gwamnati ta ga ya dace a wayar da kan matasa kan cutar, hanyoyin kamuwa da ita da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

A karshe jami’ar UNICEF Dorothy Ochola-Odongo ta ce za su ci gaba da hada hannu da gwamnati don ganin an dakike ci gaba yaduwar cutar kanjamau a tsakanin matasa.

A karshe Ochola-Odongo ta ce wannan matakin da gwamnati ta dauka ya fara aiki a jihohin Benuwai,Abuja,Kaduna da jihar Legas.

Share.

game da Author