Kada kowa ya tanka wa Saraki, a kyale shi ya ci gaba da babatun sa – Buhari

0

Fadar shugaban kasa ta roki masoyan shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada su tanka wa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kan babatu da suka da yake ta yi wa wannan mulki.

Garba Shehu ne ya saka wa takardar fadan shugaban Kasan hannu inda ya kara da cewa tun ada Saraki bai san da cewa Buhari ba zai iya ba a lokacin da suke tare yake yi masa kirari sai a yanzu.

” Shi fa Saraki ya canja ne kawai don yana neman tsayawa takarar shugaban kasa. Sannan kuma jam’iyyar da ya ke neman takarar a kai basu da abin cewa sai kawai ya maida hankali idan ba batancin Buhari ba babu abinda yake yi.

” Babu irin yaba wa Buhari da Saraki bai yi ba a baya-bayannan, Ya fadi da bakin sa cewa Buhari mutumin kirki ne, Buhari mutum ne mai cikakken lafiya, Salon mulkin sa ya cancanci yabo, duk ya fadi, amma da yake shima ya na so ya dare kujerar shugabancin Najeriya sai gashi tun kafin a kira assalatu, Saraki ya fara gaggawar nuna yunwar sa a fili.” Inji Garba Shehu

Shehu ya roki masoya Buhari da magoya bayan sa da kada su kula Saraki ballantana ma har su tanka shi.

Idan ba a manta ba, a dan kwanakinnan Buhari na shan caccaka wajen shugaban Majalisar dattawa kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP Bukola Saraki ba tare da kakkautawa.

Share.

game da Author