Idan na zama shugaban kasa zan kori duk wani Janar na soja -Sowore

0

Jagoran tafiyar siyasar ‘TakeItBack Movement’, kuma shugaban jam’iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa idan ya samu dama, zai tsige dukkan Janar-Janar na sojojin Najeriya, domin tsaro ya tabbata a kasar nan.

Cikin wata takarda da darektar yada manufofin sa ta sa wa hannu a madadin sa, Sowore wanda ke takarar shugabancin kasar nan ya ce manyan sojojin kasar nan sun kasa tabbatar da tsaro, wanda shi ne aikin da dokar kasa ta dora musu.

A cikin takardar wadda Rachel Onamusi-Kpias ta sa wa hannu, Sowore ya ce manyan Janar- Janar na sojojin kasar nan sai tara makudan kudade suke yi, ana barin kananan sojoji a cikin halin kunci.

Ya ci gaba da cewa Jana-Janar da yawa na Najeriya sun sayi kadarori masu tsada a Dubai, cikin unguwannin alfarma, abin da ya ce akwai hujjoji da dama masu nuna hakan.

“Ya zama dole mu yi tambaya, shin ina wadannan Janar-Janar na soja suke lokacin da Boko Haram suka sace ‘yan mata daruruwa suka gudu da su?

“Kuma ina wadannan sojoji suke lokacin da Boko Haram suka tako a kan kwalta a cikin Gadara da izza su ka maido ‘yan matan da suka sace har gida, bayan an biya su makudan kudade?

“Sannan dole mu yi tambaya, tunda littattafan bayanan kudade sun nuna a rubuce cewa ana kashe makudan kudade wajen tsaro, amma ana barin kananan sojoji har sai sun yi maular abinci daga hannun mutanen kauyuka.

“Zaratan sojojin mu da sauran kurata su na nuna juriya da kishin kasa, amma kuma an bar su da tsoffin kayan yaki, su kuma Janar-Janar su na hawa manyan motocin sojoji masu sulke, su na bai wa ‘ya’yan su ilmi a makarantu masu tsada a kasashen duniya, kuma fitattun likitoci na duniya ke kula da lafiyar su.” Inji Sowore.

Share.

game da Author