Hukumar SSS ta sako mai tsaron Aisha Buhari da ta tsare bisa zargin waske mata da Naira biliyan 2.5

0

A yau Alhamis da rana ne wani dan uwan mai tsaron Aisha Buhari, Farouq Baba-Inna ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa hukumar SSS ta sako dan uwan sa Sani Baba-Inna da ta tsare bisa zargin wai ya waske wa uwargidan shugaban kasan da kudade da ake bata kyauta da ya kai naira biliyan 2.5.

Farouq ya ce a yanzu haka dan uwan sa na tare da iyalen sa a gida sannan shi kuwa yana hanyar zuwa gidan don ganin dan uwan sa.

Idan ba a manta ba a ranar Juma’ar da ta gabata ne uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta sa a tsare sannan a binciki babban mai tsaron ta wato ADC din ta bisa zargin waske mata da kudi da yayi.

Wannan kudi dai kamar yadda aka fadi kudi ne masu yawa domin sun kai naira biliyan 2.5.

Aisha ta zargi ADC din nata ne da kaucewa da wadannan kudade wanda ‘yan siyasa ne suka rika bata kyauta ta hannun sa kamar yadda da zarge shi.

ADC din mai suna Sani Baba-Inna ya fada cikin wannan kamayamaya ne bayan ya musanta karbar wadannan kudade da Aisha ke zargin sa da handamewa.

Aisha ta umarci sufeton ‘yan sanda Ibarahim Idris da ya gaggauta gudanar da bincike akai.

Nan da nan kuwa sufeto janar Idris ya tasa keyar ADC Baba-Inna inda aka fara gudanar da bincike akai.

Sai dai kuma hakan su bai cimma ruwa ba domin ba a samu Baba-Inna da irin wadannan kudade ba.

Da aka binciki asusun ajiyar sa ta banki sai aka ga naira 30,000 ne ya rage a ciki sannan ko a gidan sa ma an samu naira 1,200 ne kacal da ya ajiye wa mai dakin sa kudin cefane.

Ba a dai samu komai tare da wannan bawan Allah ba. Duk da haka Aisha tace bata gamsu ba sannan ta zargi suma ‘yan sandan cewa sun hada baki ne da Baba-Inna domin cikin wadanda ake zargi da yi wa Aisha kyautar kudi har da sufeto janar Ibrahim Idris.

Ko da yake tuni idris ya karyata haka cewa babu abin da ya taba hada shi da wannan ADC da har ya bashi kudi ya ba Aisha.

Daga nan kuma sai Aisha ta fusata ta garzaya ofishin SSS, inda a yanzu haka bincike ya nuna cewa Bana-Inna na nan a tsare a wajen su.

Share.

game da Author