Hukumar Hisba ta jihar Jigawa, ta gargadi karuwan da suke tambele a jihar da su daina karuwanci ko kuma a gaggauta kama su a hukunta su.
Kwamandan Hisba na jihar Abubakar Maisoma ne ya yi wannan kakkausan gargadin a jiya Lahadi a Kirikasamma, yayin da ya ke wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN.
Ya ce daya ga cewa musulunci ya haramta karuwanci, haka kuma dokar jihar Jigawa ita ma ta haramta shi a jihar.
Daga nan sai Maisoma ya ce hukumar sa ta aika da takardar gargadin daina sana’ar a wasu gidajen karuwai a garuruwan Kirikasamma, Kwanduk, Tasheguwa, Madaci da Marma.
Ya ce an rubuta takardar ne bayan tashi daga wani taron kwamitin tsaro na jihar, wanda ya amince da fara kai farmaki a gidajen karuwan da ke fadin jihar.
Taron inji shi ya hada jami’an Hisba, ‘yan sanda, SSS da sauran jami’an tsaro.
“Mun aika wa wadannan ‘yan mata da maneman su wasikar cewa su gaggauta tuba su daina karuwanci, ko kuma duk mu kame su a hukunta su. Tilas su koma ga iyayen su, su tuba, domin mu a nan ba su da wata mabuyar ci gaba da wannan sana’a ta su.”
Discussion about this post