Gwamnatin Tarayya ta bada hutun 1 Ga Oktoba, ranar Litinin

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ranar Litinin 1 Ga Oktoba, ta zama ranar hutun murnar zagayowar Ranar ‘yancin Najeriya.

A ranar Litinin 1 Ga Oktoba ne Najeriya za ta cika shekaru 58 da samun ‘yanci.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka a cikin wani jawabi da Babban Sakataren Ma’aikatar, Mohammed Umar ya sa wa hannu jiya Alhamis, a Abuja.

Dambazau ya taya ‘yan Najeriya murnar zagayowar ranar, tare da yin kira a ci gaba da jibintar kokarin Gwamnatin Muhammadu wajen wanzar da zaman lafiya a kasar nan, tare da hadin kai a tsakanin juna.

Ministan ya kara da cewa a cikin shekaru 58 da suka shude, Najeriya ta samu gagarimin ci gaba, ba wai a rayuwar al’umma kadai ba, har ma fannin samar da ababen more rayuwar jama’a da kuma karin samun tasiri a kasashen ketare, ta hanyar inganta dangantakar diflomasiyya da kasahen waje.

Share.

game da Author