Gwamnatin Katsina ta shata wa makiyaya burtalin kilomita 905

0

Gwamnatin Jihar Katsina ta kammala shata wa makiyaya burtaloli har na kilomita 905, domin tabbatar da wanzar da zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoman jihar.

Shugaban kwamitin sasanta rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma na jihar, Abdulaziz Lawal ne ya bayyana haka a wanin taron wayar da kai ga manoma da makiyaya a Sandamu.

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Kautal-Hore ce ta shirya taron, dominn kara samar da zaman lafiya da kuma inganta zamantakewa da juna a tsakanin makiyaya da manoma.

Daga nan kuma ya kara da cewa a cikin shekara biyu kwamitin sa ya karbo shanu sama da 30,000 da barayin shanu suka sace, kuma aka damka su ga masu shanun.

Lawal ya roki makiyaya su rika kai rahoton duk wata cin iyaka da masu gona za su rika yi su na nome burtalin da aka ware domin kasancewa hanyar wucewar makiyaya da shanun su.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ta rattaba yarjejeniya tsakanin ta da gwamnatin Jihar Maradin ta Jamhuriyar Nijar wajen magance rigingimun da kuma bin diddigin gano shanun da barayi suka sace.

Share.

game da Author