Gwamnatin Jihar Neja ta kashe naira biliyan 2.6 wajen biyan hakkin ‘yan fansho 1,599

0

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ta fitar da naira biliyan 2.6 da ta biya hakkin kudaden ‘yan fansho har su 1,599 daga cikin ma’aikatan kananan hukumomi da ma’aikatan jihar.

Darakta Janar na Hukumar Fansho Usman Muhammad ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Talata a Minna.

Ya ci gaba da cewa adadin ya kudin naira biliyan 1 ga ma’aikatan gwamnatin jiha sai kuma naira biliyan 1.5 ga ma’aikatann kananan hukumomi.

Daga nan sai ya ce jimlar wadanda suka ci moriyar biyan na su hakkin sun kai mutum 1,599.

Muhammad ya ce ma’aikatan gwamnatin jiha su 456 ne yayin da na kananan hukumomi kuma su 1,14.

Ya ce an yi biyan kudaden fansho din aji daban-daban har sau hudu, amma cikon na biyar daga ma’aikatann kananan hukumomin ba a kai ga damka musu na su kudaden ba tukunna.

Share.

game da Author