Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu matakan da za su taimaka wajen inganta wuraren ajiyan kayan aiki domin asibitocin kasar nan.
Ya ce gwamnatin za ta yi haka ne ta hanyar amfani da tsarin ‘Public Private Partnership (PPP)’ tsarin hada guiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin samun nasara kan haka.
Ya fadi haka ne da yake ganawa da jami’in ICRC Chidi Izuwa a Abuja.
A lokacin da yake karban satifiket din wannan hidimar Adewole ya tabbatar wa Izuwa cewa zai yi iya kokarin sa don ganin kwamitin zantaswa ta kasa ta amince da wannan hidima ta su.
” Samar da ingantattun wuraren ajiya dabara ce da za ta tabbatar mana da ingancin kayan aikin da muke amfani da su musamman magungunan.
” Sannan hakan zai taimaka mana wurin samar da ingantatun magungunan wa asibitocin dake bukata a kasar.
Bayan haka Adewole ya ce gwamnati na shirin hada hannu da ICRC domin ganin ta samar da ingantattun asibitocin kula da masu fama da cutar daji.
Ya ce gwamnati za ta yi haka ne ta hanyar amfani da tsarin ‘PPP payment model’.
” A wannan karon kamfanoni masu zaman kan su za su biya duk kudaden da za a bukata wurin siyo kayan aikin da samar da wadannan wurare.
A karshe Izuwa ya ce tsarin PPP ta kammala shiri tsaf da kamfanoni masu zaman kan su don daukar nauyin kula da wadannan wurare da gwamnati ke kokarin samar wa har na tsawon shekaru biyar.
Ya kuma yi kira ga ministan da ya shigar da kudirin na’uran wutan lantarki dake amfani da hasken rana domin samar da wutan lantarki wa asibitocin kasar.
‘‘Hakan zai taimaka wajen inganta aiyukkan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da suke yawan famada matsalar wutan lantarki akai-akai.”
Discussion about this post