Muna kira ga gwamnati ta gaggauta ceto, Leah Sharibu – Kungiyar CAN

0

Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ceto ‘yar makarantar Dapchi da Boko Haram suka sace a Jihar Yobe.

Shugaban CAN Samson Ayokunle ya fadi haka a taron samun madafa game da kashe-kashen da sace sacen mutanen da ake yi a kasar nan wanda kungiyar ‘Ecumenism for Development and Peace Initiative, (EDAPI)’ta shirya a Abuja.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Boko Haram suka kai hari makarantar matan na sakandere dake Dapchi inda suka sace daliban makarantar wadda Leah Sharibu na cikin su.

Ita dai Leah bata dawo da ‘yan uwan ta bane a lokacin da aka dawo da su saboda wai taki musulunta.

Ayokunle ya yo kira ga gwamnati da ta gaggauta ganin an saki Leah musamman ganin yadda a cikin wannan makon Boko Haram din suka aiko da bidiyon dake nuna yadda suka kashe wani ma’aikaciyar kungiyar bada agaji na ‘Red Cross’ mai suna Saifura Khorsa tare da yi wa Leah barazanar kisa.

” Hakin gwamnati ne ta kare rayuka da dukiyoyin mutanen da take shugabanta amma yau an wayi gari gwamnatin Najeriya ta kasa dawo da sauran ‘yan matan Chibok ballantan Leah Sharibu duk da bidiyoyin da Boko Haram ke ta aikowa.

” A dalilin haka ne muke kira ga gwamnati da ta gaggauta ceto rayukan wadannan yara kafin lokaci ya kure.”

A karshe Ayokunle ya ce daga yanzu kungiyar CAN za ta fara wayar da kan mutane kan illolin aikata miyagun aiyukka kamar su shaye shayen miyagun kwayoyi,rikici, kungiyar asiri, zubar da ciki,kunan bakin wake da sauran su.

Share.

game da Author