Gambo Lawal ya koma jam’iyyar APC daga PDP

0

Gambo Lawal da ke takarar kujeran gwamnan jihar Barno a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC.

” Sanin kowa ne cewa Buhari mutum ne mai gaskiya wanda a yanzu haka shi kadai ne zai iya shugabantar kasar nan yadda ya kamata.

Lawal ya kuma kara da cewa baya fargaban amfani da tsarin amfani da daliget wajen fidda gwani da jam’iyyar APC ta dauka musamman ganin cewa shugaba Buhari bai tilasta wa jihohi kan tsarin da za su dauka ba.

” A dalilin haka ne na dauki matakin bin mutane gida gida ina wayar da su kan guje wa siyar da ko kuma jefa kuri’ar su ga wanda bai cancanta ba.

Idan ba a manta ba a shekarar 2015 Gambo Lawal ya fito takarar gwamnan jihar Barno a karkashin inuwar jam’iyyar PDP inda bayan an kada shi a zaben fidda gwani ne ya zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da shugaban jam’iyyar na jihar Barno Ali Sheriff da yi masa zagon kasa

A dalilin haka ne Lawal ya kai har kotun koli inda kotu ta dauki tsawon watani hudu kafin ta yanke hukunci.

Daga baya dai kotu ta yanke hukuncin mayar wa Lawal tikitin takarar gwamnan sa amma duk da haka Lawal ya bayyana cewa kotu ta dauki tsawon lokaci kafin ta yanke hukunci wadda a dalilin haka bai sami damar yin kamfen ba har ya fadi zaben.

Share.

game da Author