Fadar Shugaban Kasa ta maida martani ga Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda ya ce giyar mulki na diban Buhari sannan ba ya saurara wa kowa kafa.
Atiku ya ce ya fara nuna damuwa dangane da shin ko zaben 2019 zai yiwu ko ba zai yiwu a bisa adalci da gaskiya in dai Buhari na kan mulki ba.
A cikin wata hira da ya yi da AFP, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ba kamar Goodluck Jonathan ba, wanda ya mika mulki a ruwan sanyi, bayan zaben 2015. Yanzu kasar nan inji Atiku ta fada hannun wani tsohon soja kuma wanda giyar mulki ta diba wanda ba zai yarda mulki ya subuce daga hannun sa, a cikin ruwan sanyi sai an fafata da shi.”
“Sai dai kuma a cikin martanin da aka maida wa Atiku, a yau Laraba, fadar sa ta amince da cewa Buhari ya cika zare wa jama’a jan-idanu amma fa wajen hana su sata da wawuke kudin gwamnati, fadar ba ta yarda da cewa Buhari ya bari giyan mulki ta dibe shi ba.
“ Giyan mulki bata dibi Buhari ba. Sannan musamman Shugaba Buhari yayi ayyukan raya kasa a dukkan fadin kasar nan wadanda zai iya bugun kirji da su har ma ta fito sake tsayawa takarar shugaban kasa.”