El-Rufai ya nada Lawal Bello babban mai shari’a na jihar Kaduna

0

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kaduna ta amince da nadin Mai shari’a Lawal Bello sabon babban mai shari’a na jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Barnabas Bantex ne ya nada Mr Bello gidan gwamnati dake Kaduna.

Mr Bello ya maye gurbin Mai shari’a Tanimu Zailani ne da wa’adin aikin sa ya cika.

Mai martaba Sarki Lere, Abubakar Mohammed II na daga cikin wadanda suka halarci bukin rantsar da sabon jujin.

Share.

game da Author