Bashir Sati sakataren jam’iyyar APC ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye ba shine farau ba wajen siyan fom din takara daga kurkuku.
Sati ya fadi wa PREMIUM TIMES haka ne a garin Jos babban birnin jihar Filato, ranar Laraba inda ya kara da cewa Dariye zai gabatar da fom din da ya siya ranar Alhamis a hedikwatan jam’iyyar.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne alkalin babbar kotun koli dake Abuja Adebukola Banjoko ya yanke wa dariye hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru 16 bisa ga kama shi da laifin handame kudaden jihar a lokacin yana gwamnan a jihar.
Sati yace ya tuna a jihar Osun sanata Iyiola Omisore wanda kotu ta daure a kurkuku da laifin kisa ya siya fom din takara daga kurkuku.
” Omisore ya siya fom sannan ya ci zabe a lokacin da yake zaman sa a kurkuku a shekaran 2003.
A karshe Sakataren yada labaran jam’iyyar APC Yekini Nabena ya bayyan cewa shi bai ga sunana dariye ba a lokacin da ya bincika jerin sunayen wadanda suka sayi fom din takara.
” Amma ina tabbatar muku da cewa idan wani ya saci jiki ya siya masa fom din a boye ne ya san da cewa za a cire sunan sa daga cikin sunayen wadanda za su fito takara daga jihar Filato.”