A yanzu haka da yammacin yau Laraba, ana can ana gumurzu tsakanin sojojin Najeriya da Boko Haram a wani sansanin sojoji da ke Damasak a jihar Barno.
Wani jami’in sojoji ne ya bayyana haka da yammacin yau, cewa har zuwa karfe 7 na daren yanzu da ya yi sanarwar ana can ana bata-kashi tsakanin Boko Haram da sojojin.
Kakakin Yada Labaran Sojoji, Texas Chukwu ne ya bayyana haka, ya tabbatar da haka a cikin wani takaitaccen jawabi da aka yada, ciki har a shafin Facebook na tsohon kakakin yada labaran sojojin, Burgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka.
“Yanzu haka sojoji na can na gumurzu da Boko Haram wadanda suka kai hari a wani sansanin sojojin da ke Damasak da misalin karfe 6 na yammacin yau. Fadan ya yi zafi sosai a halin yanzu din nan. Sojojin su na dandana wa Boko Haram kudar su.” Haka Burgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana.
Rahotanni sun ce Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai ya kai ziyara yau Laraba a yankin.