Buhari ya dora laifin kassara Najeriya a kan manyan kasar nan

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan har ya ci zaben 2019, kuma ya kara shafe wasu shekaru hudu a kan mulki, to zai bar wa ‘yan baya ayyukan alheri masu dama da zai aiwatar.

Buhari ya ce za a ga wannan bambancin ne a lokacin da ya ke jawabi ga gungun wasu ‘yan Najeriya mazauna Amurka, a jiya Alhamis.

Ya nuna takaici da kuma da-na-sanin yadda manyan kasar nan suka bari aka kassara Najeriya a cikin shekaru 16 na mulkin PDP, ba tare da sun daga muryar kin amincewa da wannan aika-aika da aka yi ba.

“Su na ganin ana kassara Najeriya, amma ba su ce komai ba.”

Sanarwar da Kakakin Yada Labaran Buhari, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya ce a lokacin da ya ke shugabancin PTF, sun yi titina daga Lagos har zuwa Kano, Anacha har zuwa Fatakwal. Amma tun daga lokacin tsakanin 1999 zuwa 2015, ba a sake gina wasu manyan hanyoyi a kasar nan ba.

“Amma duk da haka masu fada a ji na gani, ba su tsawatar ba.” Inji Buhari.”

“Don zolaya ma har kira na ake yi da suna wai Baba mai tafiyar hawainiya. To su kuma da suka rika tafiya da sauri-sauri, ina saurin na su ya kai su?”

“Cikin 1983 sojoji sun yi juyin mulki, aka nada ni shugaba. Mun kama ‘yan siyasa mun daure wadanda suka saci kudi, muka ce kowa sai ya kawo shaidar cewa kudin na sa ne, ba na sata ba.

Amma da aka kawar da ni daga mulki, sai aka maida musu kudaden su. Masu fada aji na gani ba su ce komai ba.”

Buhari ya yi jawabi mai tsawo a wurin.

Share.

game da Author