TAMBAYA: Menene hukuncin mutumin dake hada kasaru da cikakken sallah a lokacin da yake kasaru, wato wani lokacin ya cika, wani lokacin kuma ya yi kasaru?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Ita Kasaru itace Sunnar matafiyi a cikin tafiyarsa, anfi son matafiyi yayi kasaru, don itace abinda Sunnah ta koyar, kuma tafi lada, ga sauki.
Matafiyi baya bukatar kaucewa saukin da Allah yayi masa, bin wannan saukin yafi girman lada ko da kuwa shi kadai yayi sallar.
Kin yin kasaru a lokacin tafiya kaucewa koyarwan Addini ne kuma sabawa sunnan Annabi Muhammad (SAW) ne. Idan mutum ya chakuda sallar kasaru da cika salla, to ya munana aikin sa kuma hakan abin kyamane, abin ki ne.
Amma duk da haka sallar sa tayi, kuma Allah zai karba. Allah shi ne mafi sani.